Connect with us

News

 ’Yan Fashi Sun Hallaka Matashi Yayin Da Yake Shirin Fita Sallar Asuba A Kano 

Published

on

Hukumomi a Najeriya sun tsaurara matakan tsaro da kuma sa ido sosai a birnin Kano,
Advertisements
ads

Wasu da ake zargin ’yan fashi da makami ne sun kashe wani matashi a unguwar Ɗanbare da ke Ƙaramar Hukumar Kumbotso a Jihar Kano.

AMINIYA ta ruwaito cewa Lamarin ya faru ne da safiyar Litinin, a cewar mazauna unguwar, lokacin da mutanen suka shigo gidan matashin mai suna Shuaibu Muhammad da nufin yin fashi. Shaidun gani da ido sun ce an kashe Shuaibu ne da adda, a lokacin da yake shirin fita zuwa masallaci domin sallar Asuba.

Bidiyon Dan Sanda Na Daurawa Ganduje Igiyar Takalmi Ya Janyo Ce-ce-ku-ce

Wani abokin kasuwancinsa, Haruna Nuhu Hussain, ya ce su biyun suna cikin shirin fita masallaci ne lokacin da fashin ya auku.

“Ina tare da Shuaibu a lokacin da wasu suka shigo cikin gidan. Kafin mu ankara, ɗaya daga cikinsu ya kai masa sara da adda,” inji shi.

Sai dai mazauna yankin sun ce sun samu nasarar kama ɗaya daga cikin wadanda suke zargin shugabannin fashin ne, inda suka mika shi ga ofishin ’yan sanda na Ɗorayi.

“Mutane kusan goma sun tabbatar mana cewa wanda muka kama na daga cikin wadanda suka daɗe suna addabar unguwarmu, kuma a kwanakin baya ya taba yi wa wasu fashi da makami,” inji wani mazaunin yankin da ya nemi a sakaya sunansa.

Advertisement

Ana ci gaba da fargabar tsaro a yankin, inda mazauna ke kira ga hukumomi da su ɗauki matakin gaggawa.

Ƙoƙarin jin ta bakin mai magana da yawun ’yan sandan Kano, SP Abdullahi Haruna Kiyawa, ya ci tura har zuwa lokacin kammala hada wannan rahoto.

Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending