News
Ɗalibai 420,415 Kaɗai Cikin Miliyan 1.95 Ne Suka Samu Sama Da Maki 200 A UTME – JAMB
Hukumar Shirya Jarabawar Shiga Manyan Makarantu a Najeriya (JAMB) ta ce daga cikin ɗalibai miliyan 1,955,069 da suka rubuta Jarabawar UTME a bana, ɗalibai 420,415 kaɗai ne suka samu maki sama da 200.
Hukumar ta bayyana hakan ne a cikin wata sanarwa da ta wallafa a shafinta na X (tsohon Twitter) a ranar Litinin.
’Yan Fashi Sun Hallaka Matashi Yayin Da Yake Shirin Fita Sallar Asuba A Kano
JAMB ta ce akalla ɗalibai miliyan 1.5 sun kasa cin maki 200 da ke zama ƙa’idar mafi ƙarancin da ake amfani da shi a wasu manyan makarantu.
Kididdigar da hukumar ta fitar ta nuna cewa:Ɗalibai 4,756 ne suka samu maki sama da 320,Yayin da 7,658 suka samu maki tsakanin 300 zuwa 319.
Sauran daliban kuwa sun yi ƙasa da hakan, abin da ke nuna ƙarancin sakamako a bana.
A cewar hukumar, ɗalibai 71,701 ba su samu damar rubuta jarrabawar ba, saboda matsalolin daban-daban da suka haɗa da na fasahar tantance yatsa (biometric), wanda yanzu haka ake ci gaba da bincike a kai.
JAMB ta ce za ta sanar da waɗanda suka fuskanci wannan matsala ranar da za su sake rubuta jarabawar a cibiyoyin da aka ware.
Haka kuma, hukumar ta ce an kama ɗalibai 97 da ake zargin sun tafka magudin jarrabawa kai-tsaye, yayin da ake ci gaba da bincike kan wasu 2,157 da ake zargi da aikata laifuka masu alaƙa da jarabawar.
Hukumar ta bayyana cewa har yanzu ana ci gaba da gudanar da jarrabawar ga ɗalibai makafi da kuma waɗanda ke ƙarƙashin ƙungiyar JAMB Equal Opportunity Group (JEOG).
-
News7 days agoShekara Kwana: Shekaru 24 Kenan Da Hatsarin Jirgin Sama A Unguwar Gwammaja Dake Jihar Kano
-
News3 days agoKotu Ta Daure Wani Limamin Masallacin Juma’a Wata 1 Kan Tura Bidiyon Tsaraici Ga Matar Aure A Kano
-
News5 days agoƘalubalen Da Masu Ƙananan Sana’o’i Ke Fuskanta Saboda Ƙarancin Wutar Lantarki A Kano
