News
Ƙungiyar GGOODA ta Gargadi ƴan Siyasar Najeriya akan kalaman ƙiyayya Gaban Zaɓen 2027
Ƙungiyar Good Governance Development Analyst Association (GGODAA) ta gargadi ’yan siyasa da su guji amfani da kalaman ƙiyayya, cin mutunci da tunzura jama’a yayin da ake tunkarar babban zaɓen shekarar 2027.
Shugaban ƙungiyar, Alkali Sidi Bello, Esq., ya bayyana hakan a wata sanarwa da ya fitar ranar Lahadi, 9 ga Agusta 2026, inda ya ce ya kamata ’yan takara su mayar da hankali kan manufofi, shirye-shirye da hangen nesansu, maimakon amfani da ƙabila, addini ko yanki wajen raba kan al’umma.
GGODAA ta ce kalaman ƙiyayya da tunzura jama’a na iya haifar da tashin hankali da barazana ga zaman lafiyar ƙasa, musamman yayin yaƙin neman zaɓe.
Ƙungiyar ta kuma yi kira ga jam’iyyun siyasa, kafafen yaɗa labarai da masu amfani da kafafen sada zumunta da su guji yaɗa bayanan da ka iya haifar da rikici ko rura wutar ƙiyayya.
Ta buƙaci ’yan Najeriya su zabi shugabanni bisa ƙwarewa, gaskiya, manufofi da tarihin ayyuka, ba bisa ƙabila, addini ko yanki ba.
