News
APC Na Samun Gagarumar Goyon Bayan Kano Arewa Saboda Jiga-Jigan Siyasa Uku

Jam’iyyar APC mai mulki a ƙasa na ci gaba da samun gagarumar goyon baya daga yankin Kano Arewa, inda ake kallon wasu jiga-jigan siyasa guda uku a matsayin ginshiƙan tsayuwar jam’iyyar a yankin.
Wadannan mutane sune Sanata Barau I. Jibrin, Mataimakin Shugaban Majalisar Dattawa; Murtala Sule Garo, ɗan siyasa mai tasiri; da Hon. Abba Kabir Abba (Abba Bichi), ɗan Majalisar Wakilai mai wakiltar Bichi.
Ɗalibai 420,415 Kaɗai Cikin Miliyan 1.95 Ne Suka Samu Sama Da Maki 200 A UTME – JAMB
Sanata Barau Jibrin
Barau na daga cikin ‘yan siyasa masu tarihin ayyuka a fadin Kano Arewa da ma jihar gaba ɗaya. Ya kafa ayyuka da dama a bangaren ilimi, noma da kiwon lafiya. Shi ne ya ɗauki nauyin kafa Hukumar Raya Arewa Maso Yamma (North West Development Commission) a Majalisar Dattawa har ta zama doka.
Murtala Sule Garo
Kodayake Garo bai riƙe kujera ba a yanzu, amma yana da tasiri sosai a siyasar jihar. Jama’a da dama na kallon sa a matsayin ɗan siyasar da ke da karbuwa da tasiri musamman a tsakanin matasa. Yana da kyakkyawar alaƙa da shugabannin jam’iyya tun daga matakin gunduma zuwa na jiha.
Hon. Abba Bichi
A Bichi, ana kallon Abba Bichi a matsayin shugaba da wakili na gari. Ya samu yabo wajen samar da ayyukan raya ƙasa, tallafin karatu, da kuma taimakawa al’umma da sana’o’i da aikin yi. Yana taimaka wa ‘yan majalisa da sauran ‘yan Kano wajen samun nasara a ayyukan mazabu ba tare da la’akari da bambancin jam’iyya ba.
Jagoranci Da Haɗin Kai
Wadannan jiga-jigan uku suna taka rawa wajen tsare martabar APC a Kano. A cewar masu sharhi, idan ba don haɗin kan su ba, da APC za ta fuskanci matsaloli a yankin. Sai dai, Kano Arewa na samun sauƙi fiye da sauran sassan jihar wajen fuskantar ƙalubalen siyasa saboda ƙarancin ‘yan siyasa masu kwaikwayo.
Masana na ganin cewa in har aka ci gaba da tafiya da irin wannan haɗin gwiwa, APC za ta cigaba da samun karɓuwa a jihar, musamman a zaɓe mai zuwa na 2027.
Abba Anwar ya kasance Kakakin Tsohon Gwamnan Kano, Dr. Abdullahi Umar Ganduje. Za a iya tuntubarsa ta: fatimanbaba1@gmail.com
