Connect with us

News

Bidiyon Dan Sanda Na Daurawa Ganduje Igiyar Takalmi Ya Janyo Ce-ce-ku-ce

Published

on

screenshot 20250505 174555

Wani bidiyo da ke yawo a kafafen sada zumunta ya janyo ce-ce-ku-ce bayan da aka ga wani dan sanda yana durƙusawa yana daura wa Abdullahi Umar Ganduje igiyar takalmi.

Ganduje, wanda shi ne Shugaban Jam’iyyar APC na ƙasa, yana tsaye a cikin bidiyon, yayin da dan sandan da ba a san ko wanene ba ke durƙushe yana daura masa takalmin.

Advertisement

RMAFC Ta Bukaci Gwamnatin Tarayya Ta Sake Duba ’Yancin Kananan Hukumomi

Bidiyon ya tada kura sosai a kafafen sada zumunta, inda mutane da dama ke nuna rashin jin daɗinsu da yadda dan sanda a cikin kayan aiki zai zubar da mutuncin aikinsa .

Wani mai amfani da kafar X (Twitter) mai suna @og_cemoni ya ce, “Shin zai yi wa wani dattijo da ba Ganduje ba haka? Ya kamata ya girmama kayan aikinsa, ba shekarun mutum ba.”

Advertisement

Shi kuwa @kelvin_kertz ya rubuta cewa, “’Yan sanda a Najeriya su ne masu kare talakawa a cikin takarda, amma a zahiri bayi ne ga ’yan siyasa.”

Wasu kuma na ganin watakila Ganduje ya taimaka wa dan sandan a baya, shi ya sa ya ke nuna masa ƙwazo da biyayya.

Advertisement

Amma da yawa daga cikin masu sharhi sun bayyana cewa hakan abin kunya ne ga rundunar ’yan sanda da kuma mutuncin jami’in tsaro.

Wannan bidiyon ya zo ne makonni bayan wani bidiyo da ya nuna wasu ’yan sanda suna karɓar kuɗi daga wani ɗan kasar Sin. A cikin bidiyon, an ga ’yan sandan cikin jere suna karɓar kuɗin da hannunsa.

Advertisement

Hukumar ’yan sanda ta kasa ta tabbatar da cewa an gano jami’an da ke cikin bidiyon kuma za a ladabtar da su.

Ya zuwa yanzu, rundunar ba ta ce komai ba dangane da bidiyon na Ganduje da dan sandan da ke daura masa takalmi.

Advertisement

 

 

Advertisement

 

DAILY TRUST 

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending