Politics
Jam’iyyar NNPP Ta Mutu Murus Domin Kwankwaso Na Shirin Dawowa APC – Ganduje

Shugaban jam’iyyar APC na ƙasa, Dr. Abdullahi Umar Ganduje, ya bayyana cewa jam’iyyar NNPP ta rasa kowane irin tasiri a siyasar Najeriya, yana mai cewa jam’iyyar ta mutu murus kuma babu abin da ya rage mata sai tarihin da za a tuna da ita.
Ganduje ya yi wannan bayani ne a yau Talata a birnin Abuja, lokacin da ya karɓi baƙuncin mambobin wata ƙungiyar masu goyon bayan shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu, waɗanda suka kai masa ziyarar ban girma a sakatariyar jam’iyyar APC ta ƙasa.
Gwamnatin Tarayya Ta Ayyana Ranar Juma’a da Litinin A Matsayin Ranar Hutu
Tsohon Gwamnan Jihar Kano ya bayyana cewa jam’iyyar NNPP na fuskantar matsanancin rauni kuma tana kan hanyarta ta ƙarshe, yana mai cewa: “NNPP ta kai ƙarshe, kuma nan ba da jimawa ba za ta zama tarihi a siyasar Najeriya.”
Ganduje ya kuma nuna shirinsa na buɗe ƙofa ga masu sha’awar komawa jam’iyyar APC, musamman tsohon abokinsa a siyasa, Sanata Rabi’u Musa Kwankwaso. Ya bayyana cewa idan Kwankwaso ya yanke shawarar komawa APC, zai kasance maraba da shi cikin jam’iyyar.
“Ƙofofin jam’iyyar APC a buɗe suke ga duk wanda ya fahimci gaskiya kuma ke neman dawowa gida. Idan Kwankwaso ya shirya, muna masa maraba,” in ji Ganduje.
Wannan jawabi na Ganduje na zuwa ne a daidai lokacin da ake ci gaba da hasashen yiwuwar sake hadewar manyan ’yan siyasar Kano a jam’iyya guda, domin karfafa dakarun su kafin babban zaɓ
e mai zuwa.