Politics
Shugaban Matasa Na PDP Bai Cika Aikinsa Ba – Adnan

Tsohon dan takarar Majalisar Jihar Kano a zaben 2023, Adnan Mukhtar Tudunwada, ya caccaki Shugaban Matasa na Jam’iyyar PDP, Muhammad Kadade, bisa zargin rashin yin isasshiyar adawa a kasar nan.
Adnan ya bayyana hakan ne a cikin wata sanarwa da ya fitar ga manema labarai a cibiyar PRNigeria da ke Abuja.
Gwamna Fubara Ya Mayar Da Martani Ga Tinubu Kan Dakatar Da Shi
Ya bayyana cewa shugabancin matasa na PDP bai cika aikinsa ba, musamman wajen jan hankalin matasa da kuma samar da hadin kai a cikin jam’iyyar.
Adnan ya ce, duk da kiraye-kirayen da aka yi ga Kadade domin shirya rangadin wayar da kai da kuma tallafa wa dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar, Alhaji Atiku Abubakar, bai dauki matakin yin hakan ba.
“A matsayin Shugaban Matasa, yana da muhimmanci a ce yana wakiltar muradun dukkan matasa da ke cikin jam’iyyar, amma ya taba taron wata kungiya ta matasa kuwa? Ko dai kawai yana daukar hoto tare da manyan mutane?” in ji shi.
Ya kara da cewa, “Matasan jam’iyya su ne ginshikin jam’iyyar, amma rashin yin abubuwan da suka dace ya sa reshen matasa na PDP ya zama raunana. Idan har yana son gyara kura-kurensa, to ba a makara ba, sai dai a gyara.”
Adnan, wanda kuma malami ne a jami’a da kwararre a fannin hulda da jama’a, ya bukaci matasa a duk fadin kasar nan da su hadu wuri guda domin ceto Najeriya daga halin da take ciki ta hanyar marawa kowanne yunkuri da zai kawoci gaba baya.