Connect with us

News

Gwamna Fubara Ya Mayar Da Martani Ga Tinubu Kan Dakatar Da Shi

Published

on

Siminalaye Fubara 750x430
Spread the love

 

Gwamnan Jihar Rivers da aka dakatar, Siminalayi Fubara, ya bayyana cewa tun daga lokacin da ya hau mulki, ya sadaukar da kansa wajen kare rayuka da dukiyoyin al’umma tare da inganta ci gaban jihar. Sai dai ya koka kan yadda ‘yan majalisar dokokin jihar ke kawo cikas ga kokarinsa.

A wata sanarwa da ya fitar bayan shugaban kasa, Bola Ahmed Tinubu, ya sanya dokar ta-ɓaci tare da dakatar da shi da mataimakiyarsa na tsawon watanni shida, Fubara ya jaddada cewa duk matakan da ya dauka bisa rantsuwar kama aiki ne. Ya ce bayan shiga tsakani da Tinubu ya yi, ya aiwatar da yarjejeniyar sulhu, ciki har da mayar da kwamishinonin da suka ajiye aiki.

Advertisement

Kotu Ta Ba da Umarnin Kama Tsohon Kwamishinan Ganduje

Fubara ya kara da cewa ya bi hanyoyin doka don dawo da zaman lafiya a jihar, amma kokarinsa na fuskantar turjiya daga majalisar dokokin jihar. Duk da haka, ya ce yana ci gaba da gudanar da gwamnati yadda ya kamata, yana biyan albashi kuma yana aiwatar da manyan ayyukan ci gaba.

Ya bukaci ‘yan jihar su ci gaba da bin doka da oda, yana mai cewa za su ci gaba da tattaunawa da masu ruwa da tsaki domin tabbatar da dorewar dimokuraɗiyya da bunkasar jihar.

Rikicin siyasar Rivers ya ƙara kamari ne bayan rashin jituwa tsakanin Fubara da magabacinsa, Ministan Birnin Tarayya, Nyesom Wike, lamarin da ya sa ‘yan majalisar dokokin jihar masu biyayya ga Wike suka yi barazanar tsige Fubara daga mukaminsa.

Advertisement

 

Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *