News
Falalar Kwanaki Goma Na Karshen Watan Ramadan

Watan Ramadan wata ne na rahama, gafara, da ‘yanci daga wuta. Kwanaki goma na ƙarshe suna da matuƙar falala, musamman saboda darajar da suke da ita a wajen Allah. Ga wasu daga cikin manyan falalarsu:
1. Laylatul Qadr
A cikin waɗannan kwanaki, akwai daren Laylatul Qadr, wanda yake da daraja fiye da watanni dubu. Allah Ya ambace shi a cikin Alqur’ani (Suratul Qadr: 1-5), yana cewa:
“Lalle ne, Mun saukar da shi (Alqur’ani) a daren daraja. Kuma menene ya sanar da kai menene daren daraja? Daren daraja ya fi watanni dubu.”
2. ‘Yantawa daga wuta
A cikin waɗannan kwanaki, Allah yana yantad da bayinsa daga azabar wuta. Annabi (SAW) ya ce:
“An sanya Ramadan kashi uku: farkonsa rahama, tsakiyarsa gafara, ƙarshe kuma ‘yanci daga wuta.” (Ibn Khuzaymah: 1887).
3. Sunnon I’tikaf
Annabi Muhammad (SAW) yana yin I’tikaf (zaune a masallaci) a cikin waɗannan kwanaki domin ƙara kusanci da Allah. Wannan yana ƙarfafa ibada da nisantar shagaltuwa da duniya.
4. Ƙara Ibada da Istigfari
Musulmai suna ƙoƙarin ƙara karatun Alqur’ani, azkhar, istigfari, da yin sallah cikin dare, domin neman kusanci da Allah.
5. Karɓuwar Addu’a
Addu’a a cikin waɗannan kwanaki na ƙarshe tana da tasiri sosai, musamman a daren Laylatul Qadr.
Wadanda suka yi ƙoƙari a cikin waɗannan kwanaki suna da babbar riba, kuma suna daga cikin waɗanda Allah zai yanta daga azaba. Wannan dama ce ta ƙara ƙwazo wajen ibada da neman gafara daga Ubangiji.