News
Tarihi: Yadda Aka Sauke Sheikh Abubakar Gumi Daga Shugabancin Hukumar Alhazai Ta Ƙasa A 1978
A ranar 23 ga watan Agustan shekarar 1978, gwamnatin mulkin soja ta Tarayyar Najeriya ƙarƙashin jagorancin Janar Olusegun Obasanjo ta sauke fitaccen malamin addinin Musulunci, Sheikh Abubakar Mahmud Gumi, daga muƙaminsa na shugaban Hukumar Alhazai ta Ƙasa.
A wancan lokaci, Sheikh Gumi na daga cikin manyan malaman Musulunci masu tasiri a Najeriya, musamman a Arewacin ƙasar, inda ya taka muhimmiyar rawa wajen gyaran harkokin addini da wayar da kan al’umma.
Mutuwar Ɗalibi Kan N13,500 Ta Jawo Dakatar Da Karatu Da Zanga-Zanga A Jami’ar FUTO
Sauke shi daga wannan muƙami ya jawo ce-ce-ku-ce a tsakanin mabiyansa da sauran jama’a, kasancewar yana da babban tasiri a harkokin Musulunci da kuma gudanar da ayyukan Hajji.
Sheikh Gumi ya ci gaba da kasancewa ɗaya daga cikin fitattun malaman Musulunci a tarihin Najeriya har zuwa rasuwarsa a shekarar 1992, inda ya bar gagarumar gudunmawa a fannonin ilimi, wa’azi da kuma fassarar Alƙur’ani zuwa harshen Hausa.
-
News2 days ago
Karuwar Ta’ammuli Da Miyagun Ƙwayoyi Tsakanin Mata Na Barazana Ga Makomar Iyali – Masana
-
Opinion6 days ago
Wakilcin Mataimakin Gwamna Garo A Taron Tsaro Na Arewacin Najeriya Abin A Yabawa Gwamna Yusuf Ne
-
News2 days ago
Zaben 2027: INEC Ta Amince Da Atiku Abubakar, ‘Yan Takarar ADC 470
