News
Jami’an NSCDC Sun Cafke Mutum 10 Kan Zargin Satar Kayan Gwamnati A Kano
Jami’an Hukumar Tsaro da Kare Kadarorin Al’umma ta Najeriya (NSCDC) reshen Jihar Kano sun kama mutum 10 da ake zargi da aikata laifuka daban-daban da suka haɗa da lalata kayayyakin gwamnati, sata, haɗa baki wajen aikata laifi, shiga haramtacciyar hanya da kuma karɓar kayan sata.
Hakan na kunshe ne cikin wata sanarwa da jami’in hulɗa da jama’a na hukumar a jihar, SC Ibrahim Abdullahi, ya fitar ranar Laraba.
Naira Dubu 100 Ta Yi Kaɗan, Mafi Ƙarancin Albashi Ya Kamata Ya Kai Miliyan Ɗaya — Kungiyar NLC
A cewar sanarwar, an kama waɗanda ake zargin ne a wurare daban-daban da suka haɗa da Gwarmai da ke Ƙaramar Hukumar Ghari, yankin masana’antu na Challawa, Unguwar Rimi da kuma Waratallawa a Ƙaramar Hukumar Kumbotso ta Jihar Kano.
Sanarwar ta bayyana cewa rundunar NSCDC ta jihar ta samu nasarar cafke waɗanda ake zargin ne a yayin da take ci gaba da ƙoƙarin dakile ayyukan masu lalata muhimman kadarorin gwamnati da sauran laifuka a faɗin jihar.
Kwamandan NSCDC na Jihar Kano, Commandant Mohammed Hassan Agalama, ya gabatar da waɗanda ake zargin a hedikwatar rundunar da ke Kano, inda ya bayyana cewa hukumar ba za ta yi ƙasa a gwiwa ba wajen kare kadarorin gwamnati da kayayyakin more rayuwa daga masu aikata laifuka.
Kayayyakin da jami’an tsaro suka ƙwato daga hannun waɗanda ake zargin sun haɗa da mita 200 na wayoyin aluminium, wayoyin copper, wayoyin hannu, na’urorin adana wuta (power bank) da kuma wasu makamai masu haɗari da suka haɗa da wuƙaƙe, adda, takobi da almakashi.
Hukumar ta ce ta kammala bincike kan lamarin, tare da bayyana cewa nan ba da jimawa ba za a gurfanar da waɗanda ake zargin a gaban kotu domin su fuskanci hukunci bisa laifukan da ake zarginsu da aikatawa.
Agalama ya kuma yi kira ga mazauna jihar da su ci gaba da bai wa hukumomin tsaro sahihan bayanai domin taimakawa wajen yaƙi da masu aikata laifuka da tabbatar da zaman lafiya a Kano.
