News
Naira Dubu 100 Ta Yi Kaɗan, Mafi Ƙarancin Albashi Ya Kamata Ya Kai Miliyan Ɗaya — Kungiyar NLC
Ƙungiyar Ƙwadago ta Najeriya (NLC) ta yi watsi da batun mayar da mafi ƙarancin albashi zuwa Naira 100,000, tana mai cewa adadin ya yi ƙasa matuƙa idan aka yi la’akari da halin matsin tattalin arziƙi da tsadar rayuwar da ma’aikata ke fuskanta a ƙasar nan.
Kakakin NLC, Benson Upah, ne ya bayyana hakan a matsayin martani ga sanarwar da Ƙungiyar Gwamnonin Najeriya (NGF) ta yi na cewa tana nazarin yiwuwar ƙara mafi ƙarancin albashi zuwa Naira 100,000.
Harkar Tsaro Ta Taɓarɓare A Mulkin Gwamna Abba — Gwarzo
Upah ya ce ma’aikatan Najeriya sun cancanci albashin da zai dace da yadda farashin kayayyaki da ayyuka ke ci gaba da tashi, yana mai jaddada cewa mafi ƙarancin albashi da ya kamata a biya a halin yanzu shi ne Naira miliyan ɗaya a kowane wata.
Ya ce duk wani yunƙuri na sake duba albashi ya kamata ya yi la’akari da ainihin halin rayuwar ma’aikata, musamman yadda hauhawar farashin kayayyaki da raguwar darajar Naira suka ƙara tsananta wa jama’a.
Tun da farko, Shugaban Ƙungiyar Gwamnonin Najeriya kuma Gwamnan Jihar Kwara, AbdulRahman AbdulRazaq, ya bayyana cewa gwamnoni na duba yiwuwar amincewa da sabon mafi ƙarancin albashi na Naira 100,000 domin rage raɗaɗin matsin tattalin arziƙin da ake ciki.
Ya bayyana hakan ne yayin wata ziyarar gaisuwar Sallah da gwamnonin suka kai wa Shugaban Ƙasa, Bola Ahmed Tinubu.
A cewar gwamnoni, shirin ya samo asali ne daga ƙoƙarin da ake yi na tallafa wa ma’aikata sakamakon tsadar rayuwa da hauhawar farashin kayayyaki da ke ci gaba da addabar al’umma.
Sai dai NLC ta ce Naira 100,000 ba za ta wadatar wajen biyan buƙatun yau da kullum na ma’aikata ba, tana mai kira ga gwamnati da masu ruwa da tsaki da su yi la’akari da albashin da zai dace da yanayin tattalin arziƙin ƙasar.
