News
Mutane Da Dama Sun Rasa Rayukansu, Motoci Sun Kone Yayin Da Tankar Gas Ta Fashe A Abuja

Ana cikin jimami a birnin tarayya Abuja bayan da wata tankar dakon man fetur ta fashe a gadar Karu, lamarin da ya haddasa mummunar gobara tare da kona ababen hawa da kuma asarar rayuka da dama.
Shaidun gani da ido sun bayyana cewa fashewar ta faru ne cikin sauri, inda aka ji karar fashewa har sau uku a jere. Wannan ya haddasa hargitsi da firgici, yayin da hayakin mai kauri ya lullube sararin sama, kuma jama’a suka rika kokarin tserewa domin tsira da rayukansu.
Rahotanni sun bayyana cewa gobarar ta shafi motocin da ke kusa da wurin fashewar, inda akalla motoci da dama suka kone kurmus.
Majiyoyi daga asibitoci sun ce an kai wasu daga cikin wadanda suka jikkata domin samun kulawa, yayin da hukumomin lafiya ke ci gaba da kokarin ceton rayuka.
Hukumomi Tsaro sun bukaci jama’a da su guji wucewa ta yankin domin kaucewa kara jefa kansu cikin hatsari.
Hukumomi sun yi alkawarin gudanar da cikakken bincike domin gano musabbabin lamarin da kuma daukar matakan hana faruwar hakan a nan gaba.