News
Gobara Ta Kone Sama Da Masana’antu 200 Na Sarrafa Roba A Kano
Wata gobara mai girman gaske ta tashi a kasuwar ƴan gwangwan ɓangaren ƴan roba, wadda aka fi sani da Fatima Market, da ke unguwar Dakata a ƙaramar hukumar Nasarawa, Kano. Gobarar, wadda ta faro a safiyar Laraba, ta kone fiye da masana’antu 200 kurmus, inda dukiya ta salwanta da darajarta ta kai miliyoyin naira.
Rahotanni sun nuna cewa ba a rasa rai ba, amma an samu hasarar kayan aiki da injinan sarrafa roba. Shugaban masana’antun, Alhaji Aminu Abubakar, ya tabbatar da cewa dukkannin sassan B da C na kasuwar sun lalace gaba ɗaya. A cewarsa, ba a san musabbabin gobarar ba tukuna, amma ana zargin wutar lantarki ce ta haddasa lamarin.
Mutane Da Dama Sun Rasa Rayukansu, Motoci Sun Kone Yayin Da Tankar Gas Ta Fashe A Abuja
“Ma’aikatan kashe gobara sun makara, kuma lokacin da suka iso ba su da isasshen ruwa, hakan ya sa gobarar ta ci gaba da bazuwa,” in ji Alhaji Abubakar.
Shaidu sun bayyana yadda gobarar ta bazu daga wani shago a Sashi B zuwa Sashi C, inda ta ƙara ƙarfi. Kakakin rundunar ‘yan sandan jihar Kano, Abdullahi Haruna Kiyawa, ya tabbatar da faruwar lamarin, yayin da kakakin hukumar kashe gobara, Saminu Yusuf Abdullahi, ya tabbatar da cewa har yanzu ba a gano musabbabin gobarar ba.
Hukumomi sun shawarci jama’a da su ɗauki matakan kariya don gujewa irin wannan ibtila’i a gaba.
