News
Sojoji Sun Kashe ‘Yan Ta’adda 10, Sun Ceto Mutane 101 A Katsina Da Zamfara
Dakarun Sashe na 2 tare da hadin gwiwar Rundunar Sojojin Sama na Operation Fansan Yamma sun samu gagarumar nasara wajen yaki da ta’addanci a jihohin Katsina da Zamfara, inda suka kashe ‘yan ta’adda 10 tare da ceto mutane 101 da aka yi garkuwa da su.
A cewar wata sanarwa da mai magana da yawun rundunar, Laftanar Kanar Abubakar Abdullahi Akwa, ya fitar, an aiwatar da wannan farmakin ne tsakanin ranakun 17 zuwa 18 ga watan Maris. Sojojin sun kai farmaki a gundumar Faru da ke karamar hukumar Maradun a jihar Zamfara, inda suka dakile gungun ‘yan ta’adda tare da hallaka 10 daga cikinsu.
Gobara Ta Kone Sama Da Masana’antu 200 Na Sarrafa Roba A Kano
Haka nan kuma, dakarun sun kaddamar da wani farmaki kan maboyar ‘yan ta’adda a tsaunin Pauwa da ke karamar hukumar Kankara ta jihar Katsina, inda suka samu nasarar ceto mutanen da aka yi garkuwa da su.
Wannan samame wani bangare ne na kokarin da hukumomin tsaro ke yi don ganin an dakile ta’addanci a yankin Arewa maso Yamma, tare da tabbatar da zaman lafiya da tsaro ga al’ummar yankin.
