Connect with us

News

Kotu Ta Ba da Umarnin Kama Tsohon Kwamishinan Ganduje

Published

on

Spread the love

 

Babbar Kotun Jihar Kano ta bayar da umarnin cafke tsohon Antoni Janar kuma Kwamishinan Shari’a, Barrister M. A. Lawal, bayan da ya gaza bayyana a gabanta domin fuskantar tuhume-tuhume guda huɗu da suka haɗa da karkatar da kuɗaɗe da cin amana.

A cikin shari’ar, tsohon gwamnan Kano, Abdullahi Umar Ganduje, shi ne na farko a cikin waɗanda ake tuhuma, yayin da Barrister M. A. Lawal ke matsayin na biyu. Gwamnatin Jihar Kano ce ke shigar da ƙarar.

Advertisement

Gwamnan Kano Ya Bukaci Sarakuna Da Hakimai Su Fara Shirin Hawan Sallah

A zaman kotun na ranar Litinin, lauyan masu gabatar da ƙara ya buƙaci kotu da ta ɗage zaman domin miƙa wa Ganduje takardar tuhuma, yayin da aka bayyana cewa an riga an miƙa wa Barrister Lawal sammaci amma bai bayyana ba.

Alƙaliyar shari’ar, Mai Shari’a Amina Adamu Aliyu, ta bayar da umarnin cafke Barrister M. A. Lawal bisa ƙin bayyana a kotu, sannan ta ɗage sauraron shari’ar zuwa 6 ga Mayu domin gurfanar da waɗanda ake tuhuma.

A cewar takardar tuhuma, ana zargin Ganduje da Lawal da karkatar da Naira miliyan 240 don biyan kuɗin wata shari’a ta kansu, wanda ya janyo wa Gwamnatin Jihar Kano asara. Wannan laifi ya saɓa wa Sashe na 96 da 97 na Kundin Hukunta Manyan Laifuka na Kano.

Advertisement

Baya ga wannan, ana kuma tuhumar su da bayar da bayanan ƙarya da saɓa wa amana, bisa dokokin Kano State Public Complaints and Anti-Corruption Commission Law 2008 (wanda aka yi wa kwaskwarima).

Haka kuma a wata shari’a daban, kotu ta bayar da umarnin kama Jibrilla Muhammad, Manajan Daraktan Kano State Investment and Properties Limited, bayan da ya ƙi bayyana a kotu kan tuhumar karkatar da Naira miliyan 212.3 tare da wani abokin aikinsa.

Shari’ar dai na ci gaba a kotu, inda ake jiran hukunci kan waɗanda ake tuhuma.

Advertisement

 

 

SOLACEBASE

Advertisement

 

Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *