News
Gwamnan Kano Ya Bukaci Sarakuna Da Hakimai Su Fara Shirin Hawan Sallah

Gwamnan Kano, Alhaji Abba Kabir Yusuf, ya yi kira ga Sarakunan Kano, musamman Hakimai, da su fara shirin gudanar da hawan Sallah cikin tsari da kwanciyar hankali.
Gwamnan ya bayyana hakan ne a lokacin da yake jawabi a wajen taron shan ruwan da ya shirya wa Sarakunan Kano da Hakiman su a ranar Talata a fadar gwamnatin Kano.
Kana Zubar da Ƙimar Mahaifinka A Arewa – Adnan Ga Seyi Tinubu
Ya jaddada cewa da zarar Sallah ta karato, jama’a daga ciki da wajen jihar Kano sukan fara murna, domin suna fatan ganin yadda ake gudanar da bukukuwan al’ada, musamman hawan Sallah.
Daga karshe, ya bukaci Sarakuna da Hakimai su tabbatar da cewa an shirya komai cikin lumana da walwala, domin gudanar da bikin cikin kyakkyawan tsari.