News
Kwankwaso Ya Taya Gwamnan Kano Abba Kabir Murnar Zagayowar Ranar Haihuwarsa
Jagoran Kwankwasiyya, Sanata Rabi’u Musa Kwankwaso, ya taya gwamnan jihar Kano, Abba Kabir Yusuf, murnar zagayowar ranar haihuwarsa.
A cikin sakon taya murna da ya fitar a shafin sa na Facebook, Kwankwaso ya waiwayi tsawon shekarun da suka shafe suna tafiyar siyasa tare, inda ya bayyana cewa gwamna Abba Kabir Yusuf ya rike muhimman mukamai da dama a karkashin jagorancinsa.
NYA Ta Jinjinawa Gwamnan Kano Kan Jajircewarsa Wajen Inganta Rayuwar Matasa
Ya ce Abba ya fara aiki a matsayin Mataimakinsa (PA) a zangon mulkinsa na farko da kuma lokacin da yake Minista, sannan ya zama Babban Mataimaki (PPA), daga bisani kuma Kwamishina.
Kwankwaso ya bayyana cewa wadannan mukamai sun ba Abba Kabir Yusuf damar bayar da gagarumar gudunmawa wajen aiwatar da manufofi da shirye-shiryen da aka tsara domin ci gaban jihar Kano.
Ya kuma yi masa addu’ar samun karin hikima, lafiya da tsayawa tsayin daka, tare da fatan Allah Ya ba shi cikakkiyar fahimta da hangen nesa domin ci gaba da jagorantar jihar yadda ya kamata.
-
News3 days agoWasu Ƴan Daba Sun Kai Farmaki Kasuwar Siyar Da Wayoyi Ta Farm Center Dake Kano
-
News5 days agoWasu Fusatattun Matasa Sun Ƙona Mutum Uku Har lahira A Filato
-
News5 days agoAbin Takaici Ne A Kyale Mata Su Cire Wandunan Da Aka Basu Akan Titi Suna Dagawa A Cikin Al’ummar Da Ke Alfahari Da Kunya Da Addini
