News
NYA Ta Jinjinawa Gwamnan Kano Kan Jajircewarsa Wajen Inganta Rayuwar Matasa
Ƙungiyar Northern Youth Assembly (NYA), wadda aka fi sani da Majalisar Matasan Arewa, ta yaba wa Gwamnan Jihar Kano, Alhaji Abba Kabir Yusuf, bisa jajircewarsa na inganta rayuwar matasa da ƙarfafa su su zama masu dogaro da kai a fannonin rayuwa daban-daban.
Ƙungiyar ta bayyana cewa ta kuduri aniyar ci gaba da wayar da kan matasa a Jihar Kano da sauran sassan Arewa, domin su taka rawar gani wajen ci gaban al’umma ta hanyar ilimi, ƙwarewa da shugabanci nagari.
Hukumomin Ƙasar Iran Sun Bayyana Cewa Ba Za Su Sassauta Wa Waɗanda Suke Tayar Da Tarzoma Ba
Sakataren ƙungiyar na ƙasa, Dr. Hafiz Garba, ya bayyana hakan ne yayin taron matasan Kano na yini guda da aka gudanar a ranar Litinin a Jami’ar Northwest da ke Kano.
Dr. Hafiz Garba ya ce ba za a samu ci gaba mai ɗorewa ba muddin matasa za su ci gaba da yin ƙorafi kawai, ba tare da gabatar da ingantattun hanyoyin magance matsalolin da ke addabar al’umma ba.
“Tarihi ba ya rubuta burace-burace, sai ayyuka. Wannan taro ya zama matattarar ra’ayoyi da za su koma aiki, haɗin kai da zai haifar da ci gaba, da tattaunawa da za ta taimaka wajen inganta manufofin gwamnati,” in ji shi.
An gudanar da taron ne a ƙarƙashin taken “Shimfiɗa Ajandar Ci gaban Jihar Kano.”
Da yake jawabi a matsayin babban bako, Kwamishinan Yaɗa Labarai da Harkokin Cikin Gida na Jihar Kano, Kwamared Ibrahim Abdullahi Waiya, ya yi kira ga matasa da su gina rayuwarsu bisa gaskiya, ladabi da jajircewa.
Ya ce nasarar rayuwa na buƙatar tsari, haƙuri da naci, tare da ƙarfafa gwiwar matasa da su tsara makomarsu ta hanyar tunani mai zurfi da dabaru masu ma’ana.
Taron ya samu halartar wakilai daga hukumomin tsaro da suka haɗa da DSS, Rundunar ’Yan Sanda da NDLEA, tare da malamai daga jami’o’i, shugabannin ƙungiyoyin ɗalibai, ƙungiyoyin matasa da mata, da kuma wakilan kafafen yaɗa labarai.
A ƙarshen taron, an karrama Gwamnan Jihar Kano, Alhaji Abba Kabir Yusuf, da Kwamared Ibrahim Abdullahi Waiya, tare da wasu fitattun ’yan kasuwa da shugabanni, bisa gudummawar da suka bayar wajen ci gaban matasa da inganta shugabanci a jihar
