News
Kotu Ta Tsare Shugaban Makaranta Da Malami Kan Zargin Cin Zarafin Ɗaliba A Gombe
Kotun Majistare ta 16 da ke Gombe ta bayar da umarnin tsare shugaban makarantar Destiny Treasure International School, Nasiru Barau Manu, da wani malamin makarantar, Eleazer Yila, a gidan gyaran hali kan zargin lalata da wata ɗaliba mai shekara shida.
Masu gabatar da ƙara sun shaida wa kotun cewa ana zargin Eleazer Yila da aikata laifin a watan Yulin 2026 a harabar makarantar da ke unguwar Arawa a birnin Gombe, lamarin da ya tonu bayan yarinyar ta sanar da mahaifiyarta abin da ya faru.
Jami’ar Northwest Kano Ta Gabatar da Muhimman Bayanai Kan Lafiyar Al’umma a Tofa
Haka kuma, ana zargin shugaban makarantar da ƙoƙarin yi wa lamarin rufa-rufa da kare malamin maimakon ya kai hukumomin da suka dace rahoto.
Bayan an karanta musu tuhume-tuhumen da suka shafi lalata da kuma ɓoye wanda ake zargi da aikata laifi, duka waɗanda ake tuhuma sun amsa laifin.
Lauyan gwamnati mai gabatar da ƙara, Barrista Manir Mohammed Sambo, tare da Barrista Nafi’u Abubakar da ke sa ido kan shari’ar, sun shaida wa kotun cewa laifukan sun saɓa da tanade-tanaden Sashe na 285 da na 167 na Dokar Penal Code.
Alƙaliyar kotun, Babbar Majistare Hamaira Bema Demba, ta amince da buƙatar masu gabatar da ƙara na gudanar da taƙaitacciyar shari’a.
Kotu ta kuma bayar da umarnin tsare waɗanda ake tuhumar a gidan gyaran hali, sannan ta ɗage shari’ar zuwa ranar 28 ga Yuli, 2026, domin yanke hukunci.
-
Opinion3 days ago
Wakilcin Mataimakin Gwamna Garo A Taron Tsaro Na Arewacin Najeriya Abin A Yabawa Gwamna Yusuf Ne
-
News5 days ago
Wasu Da Ake Zargi ‘Yan ISWAP Ne Da Iyalansu Sun Mika Wuya Ga Dakarun Soji
-
News2 days ago
Gwamna Abba Ya Ayyana Murtala Sule Garo A Matsayin Wanda Zai Yi Masa Takarar Mataimakin Gwamna A Zaɓen 2027
