Connect with us

News

Jami’an Ƴansanda Sun Cafke Wani Da Ake Zargin Mai Garkuwa Da Mutane Ne A Kano

Published

on

IMG 20260715 WA0001

Rundunar ‘Yan Sandan Jihar Kano ta sanar da cafke wani mutum mai suna Mohammed Isah Haruna, mai shekaru 28, bisa zargin hannu a ayyukan garkuwa da mutane da kuma kai wa ‘yan bindiga makamai da kayan sojoji.

Kakakin rundunar ya bayyana cewa an samu nasarar kama wanda ake zargin ne bayan wani ɗan ƙasa mai kishin al’umma ya kai sahihan bayanai ga jami’an tsaro cewa an ga wani mutum sanye da kayan sojoji cikin yanayi mai cike da shakku a ƙauyen Rimaye.

Kotu Ta Tsare Shugaban Makaranta Da Malami Kan Zargin Cin Zarafin Ɗaliba A Gombe

Bayan samun rahoton, jami’an ‘yan sanda tare da haɗin gwiwar al’ummar Rimawa sun kai samame cikin gaggawa, inda suka cafke wanda ake zargin. A binciken da aka gudanar, an gano wata jaka a hannunsa da ke ɗauke da mujallar bindigar AK-47 guda ɗaya mai harsasai 30, ƙarin harsasai 79 na AK-47, kayan sojoji guda biyu, hulunan sojoji guda uku, katin shaidar soja na bogi, katunan shaida daban-daban, katunan ATM guda huɗu da kuma takalman sojoji na hamada.

Rundunar ta ce yayin gudanar da bincike, Mohammed Isah Haruna ya yi ikirarin cewa ya je yankin ne domin kai waɗannan kayayyaki ga wasu ‘yan bindiga da ke buya a cikin daji. Ta ce bincike ya ci gaba domin gano sauran waɗanda ake zargi da hannu a lamarin da kuma tabbatar da dukkan bayanan da aka samu.

Kwamishinan ‘Yan Sandan Jihar Kano, CP Ibrahim Adamu Bakori, ya yaba wa al’ummar Rimawa kan kishin ƙasa da haɗin kan da suka nuna wajen bai wa jami’an tsaro bayanan sirri. Ya jaddada cewa rundunar ba za ta yi ƙasa a gwiwa ba wajen ci gaba da yaƙi da masu aikata laifuka, tare da kira ga jama’a da su ci gaba da bai wa hukumomin tsaro bayanan da za su taimaka wajen kare rayuka da dukiyoyin al’umma.

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending