Politics
Kwankwaso Ya Yi Kakausar Suka Kan Gwamnatin Shugaba Tinubu
Tsohon Gwamnan Kano kuma dan majalisar dattawa a baya, Sanata Rabi’u Musa Kwankwaso, ya zargi gwamnatin tarayya da nuna son kai wajen aiwatar da ayyukan raya kasa, yana mai cewa ana fifita yankin Kudu fiye da yankin Arewa.
Kwankwaso ya bayyana haka ne a ranar Alhamis, yayin wani taron jin ra’ayin jama’a kan sauya fasalin kundin tsarin mulki da aka gudanar a Fadar Gwamnatin Jihar Kano.
Kwamishina A Kano Ya Yi Belin Mutumin Da Ake Zargi Da Safarar Miyagun Kwayoyi Sulaiman Danwawu
Ya ce, “Yawancin hanyoyin da ke Arewa sun lalace, amma gwamnati na cigaba da aiwatar da muhimman ayyuka a Kudancin Najeriya, lamarin da ke kara nuna bambanci da rashin daidaito tsakanin yankunan kasar nan.”
Tsohon gwamnan ya bayyana damuwarsa kan yadda yankin Arewa ke fama da matsalolin tattalin arziki, tsaro da kuma rashin wadatattun ababen more rayuwa, duk kuwa da irin gudunmawar da yankin ke bayarwa wajen bunkasa kasa.
Kwankwaso ya bukaci gwamnati ta duba matsalolin yankin Arewa da idon basira, tare da tabbatar da adalci da daidaito a rabon ayyuka da albarkatu.
Taron wanda ya samu halartar wakilai daga majalisar dattawa, gwamnati, kungiyoyin fararen hula da shugabannin al’umma.
