Politics
Yanzu APC ta fara numfasawa a Kano
DAGA ABBA ANWAR
Yanzu dai a fili yake tarai cewar ci gaban jam’iyyar APC a Kano, tare da hadin kan ‘yan jam’iyya da kallon juna a matsayin ‘yan uwa tare da kare kyawawan manufofin jam’iyyar ya rataya ne kacokan kan shugaban Kasa Bola Ahmed Tinubu. Kenan samun nasarar ta ko wanin hakan a hannunsa yake da taimakon Allah.
Kwanan nan a wata ziyarar ta’ aziyyar rasuwar Alhaji Aminu Dantata, shugaba Tinubu ya yi nuni na hannunka mai sanda wanda hakan ya kara sanya kwarin gwuiwa da fatan alheri da hankoron samun nasarar jam’iyyar nan gaba a jihar. Hakan ya sa ‘yan jam’iyyar a Kano suke sowa cewar daga karshe dai an samu mafita. Kuma sun kara amincewa cewar yanzu dai kam jam’iyyar ta fara shirin fuskantar nasarori da kalubalen dake gaba.
Ziyarar Shugaba Tinubu Ta’aziyyar Dantata Ta Haɗa Kawunan Jiga-jigan APC A Kano
A wani yanayi mai ban sha’awa, a kuma karo na farko da jama’ar Kano su ka fara ganin tsohon dan takarar gwamnan Kano da mataimakinsa a takarar 2023, Nasiru Yusuf Gawuna da Murtala Sule Garo, kusa da babbar fada tun bayan faduwar zaben 2023 din.
Bilhasali ma, shi Garo an gan shi tare da manyan mutanen da su ka rako shugaban kasar a cikin jirgin shugaban kasa daga Abuja zuwa Kano. Wannan ba karamin karfin gwuiwa ya ba ‘yan jam’iyya a Kano ba.
Kuma a dai wannan ziyarar ne a ka hango Gawuna ya tsuguna wajen shugaban kasa, yayin da shugaban kasar ya kira daya daga cikin hadimansa ya na magana kan shi Gawunan. Da yake ba a kusa da wajen nake ba balle na ji me a ke cewa, amma yadda hoton ya nuna, ina ga watakila shugaba Tinubu ya na ba hadiman umarnin cewa su kawo masa Gawuna har fadar sa. In dai na karanci bayanin da hoton ke nunawa daidai.
Wannan ma shine karo na farko tun daga bayan zaben 2023 da a ka ga Gawuna da irin wannan kusanci da babbar fada. In ba daidai na fada ba a gyara min.
Ba wani abin ki ba ne, a ce zan sanar da shugaba Tinubu cewar irin wannan hannunka mai sanda da ya yi din nan ya na dauke da bayanai da yawan gaske wadanda a ke ta jiran irin su ba tun yau ba.
Shi wannan hannunka mai sanda da Tinubu ya yi ya bayar da amsar cewa to fa shi Tinubu ba fa ya manta da mutanen Kano ba ne. Wadanda su ka ba shi kuri’a sama da ta mahaifarsa, jihar Lagos lokacin zaben shugaban kasa na 2023.
Bari ma dai na shiga kai tsaye da mai karatu kan me ziyarar Tinubu ke nufi ga APC a Kano da kuma ci gaban ta. Alhamdulillah mu na da ‘yan takarar neman gwamnan jihar Kano a shekerar zabe mai zuwa ta 2027. Amma fa kadan ne daga cikin su suke da cancanta da sanin makamar aikin yin gwamna din. Shi fa mukamin gwamna ba fa wai kwarewa ba ne wajen ballagazar siyasa ko iya yaudara da cin amana ko ma gaba daya rashin sanin me shi kan sa mulki ke nufi. Matakin gwamna ya fi gaban haka nesa ba kusa ba.
Malam ka yarda ko kar ka yarda wadanda su ka cancanci kujerar gwamna a Kano fa su ‘yan kalilan ne ba su fi in kirga su da’ yan yatsun hannu na ba. Dan kar ma na batawa mai karatu lokaci, bari na jero su yanzun nan. Dukkansu su na da wasu yanayin cancanta ta wasu bangarorin iri daya. Bayan kuma kowannensu ya na da irin nasa fice a wasu bangarorin da ya tserewa ragowar.
Bari na fara da Mataimakin Shugaban Majalisar Dattawa wato Barau Jibrin. Wanda isar sa da cikar sa da batsewarsa ya ma fi karfin jihar Kano. Misali irin kokarin da ya yi wajen ganin an samar da Hukumar Ci Gaban Arewa Maso Yamma kadai ta isa ta ba shi wata gagarumar damar fada a ji a wannan bangaren namu. Musamman kan abinda ya shafi zaben shugaban kasa mai zuwa na 2027. Duk da cewar dai ita wannan hukuma ta na nan a kwance ko nakuda take yi ko me take yi ba a sani ba. Amman dai shi ya gama nasa bangaren na samar da hukumar. Allah Ya rika maka Sanata Barau!
A nawa hasashen Sanata Barau ya na da duk wata cancanta da shugaban kasa Tinubu zai iya daga masa likkafa ko ta bangaren zartaswa na gwamnati ko ta bangaren abinda ya shafi aikin majalisa. Mai karatu shi ma zai iya hasaso ire-iren mukaman da su ka fi na mataimakin majalisar Dattawa.
Ba tare da tuntuben harshe ko alkalami ba mutanen nan guda uku, Barau da Gawuna da Garo sune a halin da a ke ciki din nan su ka fi kowa duk wani mai neman kujerar cancanta. Har da wadanda su ka nuna sha’awar su a fili ko a boye a zaben da a ke fuskanta na gwamna na 2027. Sune za su iya hobbasar da a ke da bukata tare da jajircewa dan ci gaban jam’iyyar da ‘yan jam’iyyar. Kar ka dada kar ka rage.
Daga Gawuna har Garo, kowannensu ya na da karfin kirjin da zai iya fitowa a buga. Sannan kuma fa duk da haka tikitinsu na Gawuna-Garo tun na 2023, har yanzu fa da karfin sa. Kuma zai iya buga siyasar yadda a ke bukatar ta. Abin dai kawai ya danganta da yadda a ka lale katin wasan idan lokacin ya zo.
A nan mutum daya ne kacal, wato shugaba Tinubu yake da alhakin ganin karfin jam’iyyar da ‘yan jam’iyyar ya dawo jikinsu sabanin halin da a ke ciki yanzu haka. Wani babban abu da yake wuyan Tinubu shine ya ba’ yan APC na Kano abinda suke bukata idan lokacin zaben 2027 ya zo.
Ganin Gawuna da Garo kusa da gindin maganin abu ne da ya dace da halin da a ke ciki. Kuma hakan ya kara sa wa ‘yan jam’iyyar APC a Kano wani karsashi da kara kawata musu jam’iyyar cikin zuciyar su.
Amma fa wani abin lura shine, jam’iyyar APC za ta ci gaba da yin tagomashi idan shugaba Tinubu ya gane cewar dole fa sai ya saita wasu daga cikin wadanda ya ba mukami daga Kano, hanyar ficewa daga tsarin. Saboda rashin amfaninsu da kuma halin su na ko-in-kula da jam’iyya da ‘yan jam’iyya. Kwata kwata ba ma su da wani amfani ko kadan a siyasance.
Irin mutanen nan ne da ba su ma fahimci hikimar ba su mukamai ba. Ba sa yin wani abu da zai kara wayar da kan al’ummar mu kan irin ayyukan da gwamnatin Tinubu ke yi a wannan bangaren na mu.
Amman fa duk da haka akwai nagartattu a cikinsu wadanda su ka san ainihin dalilin da ya sa a ka ba su mukaman da a ka ba su. Daga cikin su wadanda su ka san me yamakata din da akwai shugaban jam’iyyar APC na jiha, wato Abdullahi Abbas, da a ka kai shi hukumar ci gaban Arewa Maso Gabas, da Baffa Babba Dan Agundi, Babban Daraktan Hukumar Kula da Nagarta da Inganci ta Kasa, da Musa Iliasu Kwankwaso, Babban Daraktan Kula da Harkokin Kudi na Hukumar Hadejia-Jama’are.
Sai kuma Sunusi Majidadi Kiru, na Cibiyar Nazari ta APC, da kuma Babban Lauyan nan, wato Sunusi Musa, wanda a ka nada shi kwanan nan matsayin shugaban Cibiyar Zaman Lafiya da Daidaito ta Kasa, da kuma Hon Yahuza, da a ka nada kwanan nan matsayin a shugaban Hukumar Samar da Nagarta ta Kasa. Kadan kenan daga cikin wadanda su ka cancanci mukaman da a ka ba su.
Kuma abu ne da yake a bayyane cewar daga cikin dukkan mutanen da a ka zaba a ka tura wakilci a Abuja, gaba dayan su ba wanda zai iya hada kafadarsa da Sanata Barau Maliya. Idan a na maganar tallafawa jam’iyya da ‘yan jam’iyya. Akwai wasu tsirari daga cikinsu wadanda amma fa tasirinsu kwata – kwata bai wuce iya wajen da suke wakilta ba. Duk fadi tashin su a iya tsukin wajen su kawai suke iya yi. Ba su da wani katabus ko a makotan garuruwan su ne. Wadanda a ka fi sani da “local champions.”
Shawara ta ga shugaba Tinubu ita ce, ya kamata ya yi “waje-road” da ire – iren mutanen da a ka ba mukamai, amma ba su san yadda za su tallafi jam’iyya da ‘yan jam’iyya ba. Kawai abinda su ka iya shine rarraba Naira Dubu Ashirin Ashirin ga ‘yan jam’iyya ko rarrabawa mutane bargon lulluba. Ko rarrabawa ‘yan jam’iyya risho na girki, saboda tsananin lalacewa.
Ya kamata shugaban kasa ya maye gurbin su da ‘yan gaske wadanda su ka san mutuncin jam’iyya da ‘yan jam’iyya. Ba masu yi wa mutane kallon bayi ba. Saboda babban aikin da ke gaban APC na nemawa shugaba Tinubu karin magoya baya lokacin zaben 2027 da a ke fuskanta.
A daidai wannan lokaci da muke ciki na sabuwar APC a jihar Kano, ya kamata shugabanni su kara bude idon su kar su fada tarkon ‘yan kankajere, marasa kishin al’umma, masu zama da shugabanni da nufin danna su a rami da masu amfani da sunan wai su manyan yan jam’iyya. Me jiya ta yi bare yau? Kodayake na san idon kowa a bude yake tarai. Kyar a ke kallon kowa a wannan sabuwar tafiya mai cike da fata na gari. In yi ta wasu “sai ma ranar.”
Ina fatan shugaba Tinubu zai ci gaba da hada kan ‘yan jam’iyya a Kano, musamman ma dai shugabanni. Kamar yadda a ka gani lokacin ziyarar sa ta kwanan nan ta yin ta’aziyyar Aminu Dantata. An ga fuskokin wadanda a ke tunanin ba sa ga miciji, a waje daya da manufa daya karkashin shugaba daya, wato Tinubu. Fatan hakan zai ci gaba da dorewa. Hakan ya zama wajibi dan ceto jihar daga kangin takura da rashin sanin makamar aiki.
Na ji dadin ganin muhimman mutane irin su Sanata Barau Jibrin da shugaban jam’iyya na jiha Abdullahi Abbas da Nasiru Gawuna da Murtala Garo da Baffa Babba Dan Agundi da Hon Alhassan Ado Doguwa da Sanata Kawu Sumaila da Hon Kabiru Alhassan Rurum da sauran su karkashin inuwa daya ta shugaba Tinubu lokacin wannan ziyara. Dan kara tabbatar da cewa har yau har gobe ruwan APC na maganin daudar jam’iyyun adawa.
Har yanzu kuma har gobe na yarda da cewar ya zama dole a fara kula da yan soshiyal midiya (social media) din mu idan da, ba a yin yadda ya kamata. Su ma fa mutane ne kamar kowa kuma masu muhimmanci a wannan tafiya. Alhamdulillah dai akwai wanda ya yi fice wajen kyautata musu daga lokaci zuwa lokaci. Allah Ya saka da alheri. Muhimmancinsu ya wuce duk yadda a ke tsammani.
Na yarda da cewar da irin wannan kulawa ta Tinubu ga manyan APC yanzu a Kano, ta tabbata cewar jam’iyyar ta kusa yin wani numfashi mai ban ta’ajibi da sambarka.
