Connect with us

News

‎Ziyarar Shugaba Tinubu Ta’aziyyar Dantata Ta Haɗa Kawunan Jiga-jigan APC A Kano ‎

Published

on

1752875321855

DAGA ABBA ANWAR, KANO

‎Ziyarar da Shugaban Najeriya, Bola Ahmed Tinubu, ya kai domin yin ta’aziyya ga iyalan marigayi Alhaji Aminu Alhassan Dantata a Kano, ta kasance wata kafa ta haɗin kai da zaman lafiya tsakanin manyan jiga-jigan jam’iyyar APC da ke fuskantar sabani a jihar.

Advertisement

Shugaban ya sauka a filin jirgin saman Malam Aminu Kano da yammacin Juma’a, inda ya wuce kai tsaye zuwa gidan marigayin da ke unguwar Koki. Dubban mutane sun tarbe shi da farin ciki da rera wakokin yabo, yayin da wasu ke ɗaga hotunansa da tutocin APC, alamar maraba da girmamawa.

Yan Sanda Sun Haramta Gangamin Murnar Haihuwar Peter Obi A Kaduna

A na ta mamakin wace irin dabarar mulki ko siddabarun kwarewa a ka yi amfani da shi wajen samun nasarar wannan ziyara ta ta’aziyya ba tare da wata matsala ba ko kadan. Sai a ka gano cewar hankalin shugaban kasa tabbas ya karkato jihar Kano yanzu fiye da a baya.

Advertisement

‎Ziyarar ta jawo hankalin masu lura da al’amuran siyasa, musamman ganin yadda ta bai wa shugabannin APC da ke sa-in-sa ta fili ko ta boye a tsakaninsu damar zama a wuri guda, cikin yanayin kwanciyar hankali. Wasu na kallon hakan a matsayin wata sabuwar dama ga jam’iyyar don dawo da zaman lafiya, a daidai lokacin da ake shirin fuskantar babban zaɓe a 2027.

‎Wani lamari da ya jawo muhawara shi ne bayyanar Murtala Sule Garo – wanda ya kasance mataimakin dan takarar gwamna a 2023 – cikin tawagar ‘yan rakiyar Shugaban Ƙasa, da su ka taho tare da shugaban kasa a jirgi daya, duk da cewa ba shi da wani mukami a gwamnatin tarayya. Wannan ya ƙara samar da wata nutsuwa a fagen siyasar Kano.

Advertisement

‎Haka kuma an ga fitattun jiga-jigan siyasa kamar Sanata Barau Jibrin, Mataimakin Shugaban Majalisar Dattawa; Sanata Abdurrahman Kawu Sumaila; da Nasiru Yusuf Gawuna, tsohon mataimakin gwamna, kuma dan takarar gwamna a zaben 2023. Sauran sun hada da Hon. Alhassan Ado Doguwa, Hon. Abubakar Kabir Abubakar – shugaban kwamitin kasafin kuɗi a Majalisar Wakilai – da Hon. Baffa Babba Dan Agundi.

‎Shugaban jam’iyyar APC na jihar Kano, Prince Abdullahi Abbas, da shugabannin jam’iyyar daga matakin mazaba zuwa kananan hukumomi har zuwa jiha duk sun hallara domin tarbar Shugaban Ƙasa.

Advertisement

Hakazalika, an hangi tsohon dan majalisar tarayya na Tarauni Hafizu Kawu tare da abokin hamayyarsa Nasiru Bala Ja’o’ji da magoya bayansu – alamar rage tsamin rikicin da ya dade yana raba kawunan jam’iyyar. Kuma an ga yadda kowannensu ya tara mutanen sa dan zuwa tarbar shugaban kasa Tinubu.

‎Masu fashin baki na ganin ziyarar na nuna ƙwarewar shugabanci da kwarewar sulhu da Shugaba Tinubu ke da ita, wajen sasantawa da ɗinke baraka a jam’iyya. Wasu ma na kallon hakan a matsayin wata sabuwar dama da za ta taimaka wajen dawo da martabar APC a Kano fiye da sauran jihohin Arewa maso Yamma gaba ɗaya.

Advertisement

Sannan kuma wasu masu fashin bakin na da ra’ayin cewa tabbas Shugaba Tinubu kadai na iya daidaita duk wani sabani da ke tsakanin ‘yan APC a jihar Kano.

‎Bayan kammala ziyarar, Shugaban Ƙasa ya koma kai tsaye zuwa filin jirgi, inda ya tashi zuwa Abuja da jirgin fadar shugaban ƙasa.

Advertisement

‎Allah Ya jikan marigayi Alhaji Aminu Alhassan Dantata. Ya kara jaddada Rahama gare shi.

 

Advertisement

Anwar ya rubuto wannan daga Kano

Jumma’a, 18 ga Juli, 2025

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending