Connect with us

News

An Kama Wani Tsohon Fursuna Da Zargin Damfarar Mata 17 A Kano

Published

on

IMG 20250719 WA0011

Rundunar ’Yan Sandan Jihar Kano ta cafke wani matashi da ake zargi da damfarar mata da sunan bayar da tallafin gwamnati, inda yake kwace musu wayoyin salula.

Kakakin rundunar, SP Abdullahi Haruna Kiyawa ne ya bayyana hakan a cikin wata sanarwa da ya fitar ranar Asabar, 19 ga Yuli, 2025.

Advertisement

‎Ziyarar Shugaba Tinubu Ta’aziyyar Dantata Ta Haɗa Kawunan Jiga-jigan APC A Kano ‎

A cewar sanarwar, wanda ake zargin mai suna Mohammed Usman, ɗan shekara 27 mazaunin unguwar Kofar Wambai da ke cikin birnin Kano, ya kira wata mata daga unguwar Ahmadiyya Brigade da sunan za a ba ta tallafi daga gwamnati, amma daga bisani ya yaudare ta ya sace mata waya.

Bayan cafke shi, wasu mata guda 17 sun bayyana cewa su ma ya yaudare su da irin wannan dabara ta zamba.

Advertisement

Rundunar ta kara da cewa Mohammed Usman tsohon ɗan fursuna ne, inda a baya aka daure shi na tsawon shekaru biyu ba tare da zabin biyan tara ba.

Bayan bincike, ’yan sanda sun kuma kama wasu mutane uku da ake zargi da karɓar wayoyin da aka sace daga hannunsa, tare da kwato wayoyi guda takwas.

Advertisement

Kwamishinan ’Yan Sanda na Jihar Kano, CP Ibrahim Adamu Bakori, ya bukaci al’umma da su rika lura da duk wani kira ko saƙo daga mutane da ba a sani ba, musamman masu yin alkawarin tallafi, domin kauce wa fadawa hannun masu aikata zamba da damfara.

 

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending