News
Jirgin Sama Ya Kama da Wuta Yayin Tashi a Amurka
Wani jirgin kamfanin Delta Airlines ya gamu da matsala yayin da ɗaya daga cikin injinansa ya kama da wuta daidai lokacin da jirgin ke shirin tashi daga filin jirgin sama na birnin Los Angeles (LA), a ƙasar Amurka.
Lamarin ya faru ne a safiyar Lahadi, inda jirgin mai lamba Boeing 767-400, wanda ke kan hanyarsa zuwa birnin Atlanta, ya fuskanci matsala ta fashewar wuta a gefen hagun jirgin, lamarin da ya tilasta matuƙan jirgin yin gaggawar dawowa da kuma sauka lafiya ba tare da asarar rai ko raunata kowa ba.
Bidiyon da aka ɗauka ya nuna yadda wuta ke tashi daga injin jirgin yayin da yake ƙoƙarin hawa sama. Josh, ɗaya daga cikin masu shahararriyar tashar YouTube mai suna LA Flights, ne ya ɗauki bidiyon daga farkon tashin har zuwa lokacin da jirgin ya koma filin jirgin.
Kamfanin Delta ya tabbatar da faruwar lamarin, inda ya bayyana cewa an bi duk matakan kariya da ka’idojin tsaro, kuma an sauke fasinjoji lafiya.
Hukumar kula da zirga-zirgar jiragen sama ta Amurka (FAA) ta ce za ta gudanar da cikakken bincike don gano musabbabin kamawar wutar a cikin injin jirgin.
