Connect with us

News

‎Iqra’a Academy Ta Shirya Taron Yaye Dalibai A Nguru

Published

on

IMG 20250720 WA0009

Makarantar Iqra’a Academy for Science and Islamic Education, da ke Kadawa Daki Tara, Sabon Gari Kanuri Ward, Nguru, Jihar Yobe, ta shirya babban taron yaye dalibai na shekarar karatu ta 2025, wanda za a gudanar a ranar Lahadi, 27 ga Yuli, 2025 da ƙarfe 9:30 na safe.

Taron, wanda aka tsara zai gudana a harabar makarantar, zai kunshi muhimman abubuwa da suka haɗa da karatun Alƙur’ani da kuma yaye daliban Nursery, Firamare, JSS da SS 3, da kuma bayar da lambobin yabo ga dalibai da suka nuna ƙwazo a fannoni daban-daban.

Jirgin Sama Ya Kama da Wuta Yayin Tashi a Amurka

‎Haka zalika, ana sa ran manyan baki za su gabatar da jawaban ƙarfafawa da nuni da muhimmancin ilimi, tare da gudanar da wasannin kwaikwayo da nishaɗantarwa daga ɓangaren dalibai.

‎A wata takardar gayyata da Shugaban Makarantar, Malam Adamu Rabi’u, ya fitar, ya bayyana cewa ana gayyatar iyaye, malamai, shugabannin al’umma da daukacin jama’a masu sha’awar ci gaban ilimi da tarbiyya, domin halartar wannan biki mai ɗauke da darussa da gagarumar mahimmanci.

‎Ya ƙara da cewa, “Wannan biki wata dama ce ta ƙarfafa gwiwar dalibai da tabbatar da cewa iyaye da malamai sun ci gaba da taka muhimmiyar rawa wajen ganin an samu al’umma mai ilimi da ɗa’a.”

‎A cewar shugabannin makarantar, an tanadi tsari mai kyau da tabbatar da tsaro da jin daɗin dukkan mahalarta, tare da fatan ganin kowa ya halarci taron cikin kwanciyar hankali da nishadi.

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending