News
Iran Ta Ce Ba Za Ta Halarci Taron Tattaunawa Da Amurka A Pakistan Ba
Hukumomin Iran sun ce izuwa yanzu basu cimma matsaya kan ko ƙasar za ta sake halartar zagaye na biyu na tattaunawarsu da Amurka ba, wacce za ta gudana a Islamabad babban birnin Pakistan.
Mai magana da yawun ma’aikatar kula da harkokin wajen Iran, Esmaeil Baqaei ne ya sanar da hakan, a lokacin da ya ke gabatar da taron manema labarai na mako mako.
Jam’iyyar APC Ta Sanar Da Kudin Sayen Fom Din Tsayawa Takara A Zaben 2027
Ya zuwa yanzu, ba mu da wani shiri na shiga zagaye na gaba na tattaunawa, kuma ba a yanke shawara kan wannan batu ba.
A ranar 21 ga wannan watan ne dai yarjejeniyar tsagaita wuta da ɓangarorin Iran da Amurka suka cimma za ta kawo ƙarshe, wani lamari da ke nuna cewar akwai yuwuwar a sake komawa fagen daga, idan har ba a sake cimma yarjejeniyar dindin koma sake ƙulla wata ta tsagaita wuta ba.
Iran dai ta zargi Amurka da saɓawa yarjejeniyar tsagaita wuta da suka cimma, ta hanyar datse mata jiragen ruwa da kuma kai musu hari.
Haka nan kakakin ma’aikatar wajen Iran ɗin, ya ce Amurka ta ce ba a sanya yarjejeniyar tsagaita wutar Lebanon cikin tattaunawar ta su ba, wanda ta ce hakan ba gaskiya bane, don haka ta ce a sanar da Pakistan wacce ke shiga tsakanunsu waɗannan matsalolin da aka samu.
A nata ɓangaren, Amurka ta ce mataimakin shugaban ƙasar JD Vance ne zai jagoranci tawagar ƙasar don halartar tattaunawar Islamabad, sannan itama Pakistan ta ce ta na da ƙwarin gwiwar samun halartar ɓangarorin biyu a wannan zama.
-
News5 days ago
KANO: Yara 24 Da Ake Tuhuma Da Laifi Sun Amfana Da Shirin Gyaran Tarbiya Maimakon Hukuncin Kotu A Watan Yuli
-
News4 days ago
ICPC Ta Wanke Femi Gbajabiamila Daga Zargin Badakalar Hukumar Bogi
-
News7 days ago
Gwamnatin Tarayya Ta Ba Jami’o’i Da Kwalejoji Umarnin Korar Ɗalibai Da Ke Da Alaka Da Laifin Garkuwa Da Mutane
