News
Shugaba Tinubu Bai San Mawuyacin Halin Da ‘Yan Najeriya Ke Ciki Ba —Hakeem Baba-Ahmed
Shugaban Jam’iyyar PRP, Hakeem Baba-Ahmed, ya soki Shugaban Ƙasa, Bola Ahmed Tinubu, yana mai cewa gwamnatin sa ta yi hannun riga da hakikanin matsalolin da ‘yan Nijeriya ke fuskanta.
Baba-Ahmed ya bayyana hakan ne yayin wata hira da ya yi a shirin safiya na ‘ARISE News Channel’ a ranar Litinin, inda ya ce yadda shugaban ƙasar ke kimanta aikin gwamnatinsa bai yi daidai da yadda rayuwar ‘yan ƙasar take a zahiri ba.
Kotun Ɗaukaka Ta Umarci A Kawo Sheikh Abduljabbar Domin Ya Kare Kansa A Kano
Ya kuma soki wasu kalamai da aka jingina wa Shugaba Tinubu, inda aka ce ya bayyana cewa, masu sukar gwamnatinsa suna buƙatar “sabbin gilashi” domin ganin nasarorin da ya samu ko kuma son zuciya ne ya rufe idanuwansu.
“Idan shugaban ƙasa zai ce idan ba ka ga cigaban da ya samu ba, to kana buƙatar saka sabbin gilashi ko kuma kana da son zuciya fiye da kima, ina ganin hakan, babbar abin damuwa ce,” in ji shi.
A cewarsa, yana da wahala a haɗa ikirarin cigaban da gwamnati ke yi da halin talauci da matsin tattalin arziki da ake fama da su a ƙasar.
