Connect with us

Politics

Gyaran Kundin Tsarin Mulki: Yadda Shafin Facebook na DSP Barau Ya Jawo Hankalin Jama’ar Arewa maso Yamma

Published

on

1753571311533

DAGA ABBA ANWAR 

‎Tuni al’ummar yankin Arewa maso Yamma suka bayyana gamsuwarsu da yadda Mataimakin Shugaban Majalisar Dattawa kuma Shugaban Kwamitin Gyaran Kundin Tsarin Mulki, Sanata Barau I. Jibrin, CFR, ke gudanar da muhimmin aikin da aka dora masa a matsayin wakili na kwarai da ya amince da ƙaddamar da jin ra’ayoyin jama’a kan sauya wasu sassa na kundin tsarin mulki na Najeriya.

Advertisement

‎A ranar Asabar, 26 ga watan Yuli, 2025, Sanata Barau ya wallafa wani rubutu a shafinsa na Facebook, yana bayani kan buɗe taron jin ra’ayin jama’a na yankin Arewa maso Yamma da aka shirya a jihar Kano. Daga cikin sa’o’i kaɗan bayan wallafar, an samu ɗumbin martani daga jama’a, inda fiye da mutane dari uku suka nuna goyon baya ta hanyar like, sannan sama da mutum 300 suka yi tsokaci cikin kalmomin yabo, addu’a da fatan alheri.

An Cafke Matasa 60 Bisa Zargin Ta’ammali Da Miyagun Ƙwayoyi

‎Haka zalika, kimanin mutum 300 sun raba wallafar, lamarin da ke nuna karɓuwar Sanata Barau a zukatan al’umma, musamman matasa da ke kallon sa a matsayin gwarzon shugabanci a Arewacin Najeriya.

Advertisement

‎Wasu daga cikin masu tsokaci sun haɗa da Abdullahi Bala Dawakin Tofa, wanda ya ce: “Masha Allah. Allah ya kare ka, ya taimake ka”, yayin da Usman Yareema ya kara da cewa “My boss.”

‎Safwan Ishaq ya bayyana DSP Barau da kalmomi masu nauyi, inda ya ce: “Ba wai Sanatan Kano ta Arewa ne kadai ba, kai Sanatan Najeriya ne.” Wannan na nuni da yadda wakilcin Sanata Barau ke samun karɓuwa ba a matakin mazabarsa kaɗai ba, har ma da ƙasa baki ɗaya.

Advertisement

‎Engineer Muhammad Khalid ya kira shi da “Jagora”, yayin da wasu suka ce “Shugaba ne da ke jagoranci da misali”, a wata alama ta girmamawa da yaba da nagartaccen shugabanci.

‎Barau Foreign Scholars, wata ƙungiyar dalibai da ke a kasashen waje, sun bayyana cewa: “Wannan shi ne shugabanmu kuma jagorammu.”

Advertisement

‎Taron jin ra’ayoyin jama’a da aka fara a jihar Kano, wanda za a shafe kwana biyu ana gudanar da shi, ya samu halartar wakilan jihohin Arewa maso Yamma guda bakwai, ’yan majalisar tarayya, sanatoci da wakilan gwamnatocin jihohi. A cewar DSP Barau, taron na cikin jerin taruka shida da aka gudanar a jihohin Enugu, Jos, Lagos, Ikot Ekpene da Maiduguri a ranar 4 da 5 ga Yuli, 2025.

‎Sai dai taron na Kano ya samu jinkiri domin girmama rasuwar fitaccen attajiri, Alhaji Aminu Dantata, da tsohon shugaban kasa Muhammadu Buhari, GCFR.

Advertisement

‎DSP Barau ya ce: “A madadin kwamitin Majalisar Dattawa da ke duba yi wa Kundin Tsarin Mulki na 1999 kwaskwarima, ina maraba da ku zuwa wannan taron jin ra’ayoyi na yankin Arewa maso Yamma. Wannan muhimmin mataki ne da zai tabbatar da shigar kowa cikin tsarin.”

‎Ra’ayoyin da jama’a ke bayyana a kafafen sada zumunta, musamman Facebook, sun nuna irin yadda al’umma ke kallon Sanata Barau a matsayin wakili na gaskiya, wanda ya cancanci amincewa da dogaro a kan manyan batutuwan da suka shafi rayuwar al’umma.

Advertisement

‎Wasu na ganin irin wannan karɓuwa da yabo daga al’umma na nuna cewa Sanata Barau na kan hanya mai kyau wadda ka iya zama jigo a siyasar Najeriya nan gaba, musamman da aka fara hasashen tasirin sa a zaɓen 2027 mai zuwa.

‎A zamanin da ake fuskantar ƙalubale da rashin amincewa da shugabanni a Najeriya, martanin jama’a ga DSP Barau na nuni da cewa akwai sauran shugabanni na gari da ke aiwatar da ayyukansu da gaskiya, kishin ƙasa da kulawa da muradun talakawa.

Advertisement

‎Masana na ganin cewa domin tabbatar da haɗin kai da ci gaban dimokuraɗiyya a Najeriya, akwai bukatar samun irin su Sanata Barau Jibrin a muƙaman da za su tsarkake tsarin mulki da inganta tafiyar da ƙasa.

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending