Connect with us

Politics

Sanata Barau, Laluben Ruhin APC a Arewa da Manufofin Al’umma

Published

on

FB IMG 1753978054183

DAGA ABBA ANWAR 

Kasancewar tasowar Mataimakin Shugaban Majalisar Dattawa ta Kasa kuma Mataimakin Kakakin Majalisar ECOWAS Na Daya, Sanata Barau Jibrin na zama daya daga cikin yan siyasar da ke damawa a kasar nan, ba wani abu ne na tankiya ko ja-in-ja ba. Wannan abu a fili yake ga kowa da kowa.

Advertisement

Daga samun wannan matsayi nan da nan ya zama daya daga cikin muhimman yan siyasa a jihar Kano. Tare kuma da kara samun jituwa tsakaninsa da jiga-jigan yan siyasa a jihar. Wanda hakan ba wai wani abu ne da kawai ya kamata ba. A’a abu ne wanda yake lallai don ci gaban jam’iyyar a jihar da na Arewa baki daya.

SKY Ya Bukaci Gwamnati Ta Mayar Da Hankali Kan Rage Talauci A tsakanin Al’umma

Duk da cewar taimakon sa da kuma tausayin sa ga al’ummar sa ya karade jihar gaba daya da ma wasu sassa na Arewacin Najeriya, hakan bai sa ya yi wurgi da ainihin mazabarsa ta Kano ta Arewa ba. Za a iya yi masa kallon Sanata mai tauna taura sama da biyu ma. A yanayin mu’amalarsa.

Advertisement

In har da gaske shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ya na son ya rike kuri’un da ya samu daga Arewa kuma ya ma samu kari kan hakan ya zama abin sha’awa a samu wata kafar yabawa shugabanni irin su Sanata Barau kan irin yadda suke fadi-tashi wajen hidimtawa al’umma da kuma jam’iyya. Kuma kamar yadda kokarin sa ya ma wuce jihar Kano, haka nan alfarmar da yake da ita daga al’umma ita ma ta wuce jihar Kano din.

Duk da cewar Sanata ba shine kadai mutumin da yake da damar jawo alheri ga jam’iyyar APC ba a jihar Kano da sauran wurare, amman dai tabbas ya na daga cikin jiga-jigan tafiyar. Wadanda bai kamata a wofantar da irin kokarin da su ke yi ba.

Advertisement

Ga mai karatu, ina son bayyana cewa akwai wani bincike da na yi da wasu kwararru kan tasirin ire-iren ayyukan da Sanatan ke yi a cikin al’umma. Wannan bincike kwanan nan za mu fitar da sakamakon sa, dan yi wa jama’a bayani cikakke kuma sahihi ta yadda tasirin wannan bawan Allah yake a Arewacin Najeriya.

Daga can mazabarsa ta Kano ta Arewa akwai wasu jiga-jigai wadanda su ma sun yi fice wajen tallafawa jam’iyya da yan jam’iyya. Kamar yadda yake a jihar gaba dayanta da kuma kewayen jihar.

Advertisement

Daga cikin irin wadannan mutane, akwai wadanda karfin su gaba daya bai wuce yan wuraren da suke da iko ba. Wanda hakan shi ma abin so ne kwarai da gaske. A daidai lokacin da kuma wasu jiga-jigan su na da fada-a-ji a dukkanin sassan jihar a kananan hukumomi 44 din nan. Su ma irin wadannan muhimmancinsu ya kai ya kawo. Kuma ababen so ne a kowace gaba ta mu’amalar yau da kullum.

Ta bangaren manufofin al’umma dan cigaban kasa kuma, ya kamata a yi la’akari da ire-iren nauye-nauyen da ke kan wannan Sanata, abu ne wanda yake yin su dan cigaban kasa bisa doron kishin kasa da ci gaban kasa da kuma cigaban jam’iyyar gaba daya. Wanda hakan kuma ya na da tasiri na kai – tsaye wajen nemo ruhin jam’iyyar a Kano da Arewacin Najeriya. Musamman yadda babban zabe ke tunkarowa.

Advertisement

Na tabbatar za a yarda da ni idan na ce duba da yadda Sanata yake hubbasa wajen ayyukan sa na majalisa, da irin yadda ba a kasa a gwuiwa wajen yin maganganu masu ma’ana yayin da majalisar ke zama da kuma kullum kasancewarsa daya daga cikin masu nuna kishin su na kasa da cigaban al’ummar su, to lallai mutum ne da ya cancanci yabo da jinjinawa wajen ganin an kara samun dunkulalliyar kasa.

Kamar kuma yadda nake da wasu bayanai da na samu kan yadda yake kokarin kara hada kan yan kasa dan cigaban kasar, kowa ya san harkar sa ta kishin kasa ba wasa ba ce kuma ba abar wurgi ba ce. Za mu iya yi masa kallon dan kishin kasa sahihi mai burin ganin an samu cigaba mai dorewa.

Advertisement

Ba tare da tsoron samun tuntuben alkalami ba, zan iya cewa Sanata Barau ya na samun wata kariya ne daga Allah. Wanda hakan ya sa ya samu yin zarra fiye da wasu a harkokin siyasar kasar nan.

Yadda na fahimce shi a matsayin wani ginshiki kuma wata cibiyar samun nasarar jam’iyyar APC a Arewacin Najeriya idan zabe na 2027 ya zo, zan iya cewa, yadda mu’amalar sa take tare da yadda yake kara karfafa jam’iyyar a dukkan matakai ta sa ya zama wani turke mai karfin bangazar yan adawa marasa kishin al’ummar su. Ina fatan mai karatu zai fara zuwa ya gano yadda yake mu’amalarsa kafin mutum ya yanke hukunci a kan sa.

Advertisement

Kuma tsagwaron kishin kasa da son hadin kan al’ummar kasar sune muhimman abubuwan da ya sa a gaba. Shi ya sa ma a kullum zancen sa bai wuce na a manta da wasu banbance-banbance dake tsakanin al’umma ba, saboda samun hadin kai da fuskantar kalubalan rayuwa a hade gaba daya.

Ni dai tun daga dawowa mulkin dimokuraɗiyya a shekarar 1999, zuwa yanzu ban ga Mataimakin Shugaban Majalisar Dattawan dake da tsinkaye gami da kishin dukkan bangarorin kasar nan ba kamar shi. Hakan kuma sai ya jawo masa soyayyar mutane daga bangarorin kasar nan da dama. Musamman daga Arewacin kasar.

Advertisement

Idan kuma ka duba ire-iren kudurorin da ya gabatar a gaban majalisa har su ka zama dokoki, akwai wasu daga ciki da ba a Arewacin kasar amfanin abin zai kasance ba. Sun tsallake zuwa wasu bangarorin kasar nan har can ma kudancin kasar. Hakan ta sa yake da kima a dukkan bangarorin Kasar nan.

Ga kadan daga cikin ire-iren kudurorin da ya gabatar har su ka zama dokoki nan a bangarorin kasar nan. Misali akwai “Cyber Crimes (Prohibition, Prevention, etc) Bill (2023), Federal College of Education (Technical), Aghoro Bill (2019), in Bayelsa state, College of Mines and Geological Studies, Guyuk, Bill (2019), Federal University of Aquatic Studies, Ogharu, Bill (2019), in Anambra state and University of Maritime Studies, Oron, Bill (2017), Development Planning and Projects Continuity Bill (2023),” da sauran su.

Advertisement

Wadannan dalilan da ma wasu da dama sun nuna cewar wannan mutumin dan kishin kasa ne gangariya.

Ba zan taba mantawa ba, a can baya da a ka yi mataimakan shugabannin majalisar dattawa ta kasa, an yi wasu irin mutane ne wadanda ba su ma damu da su dinga tallata kyawawan ayyukan gwamnatocin jam’iyyunsu masu mulki ba.

Advertisement

Wasu ma daga cikin irin su ba wai kawai rashin yin hobbasar samarwa jam’iyyunsu farin jini ba, sai ma kawai su ka zama sanadin jawowa jam’iyyun nasu zagi da kushewa ta ko ina. Sai su ka zama tamkar ‘ya’ yan kuka din nan da a ke cewa.

To ka ga dai banbancin dake tsakanin Sanata Barau da wasu daga cikin wadanda su ka taba rike shugabanci a Majalisa irin nasa. Ba kuma fa wai ina kalubalantar kowa ba ne, amma dai ni gaskiya har yanzu ban ga Mataimakin Shugaba Majalisar Dattawa na Kasa da ya yi irin na Sanata Barau ko makamancin irin nasa ba. Idan kuma da gyara a gyara min.

Advertisement

Anwar ya yi wannan rubutun ne daga Kano

Alhamis, 31 ga Juli, 2025

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending