Politics
Ra’ayin Minista Ata Kan 2027 A Kano : Tawa Mahangar
DAGA ABBA ANWAR
Ya kamata ga mutane su fahimci cewar, maganar da Karamin Ministan Gidaje, Yusuf Abdullahi Ata ya yi kan yadda jam’iyyar APC za ta samu nasara a zaben dake gaban mu na 2027, ra’ayin sa ya fada na yadda yake ganin za a kai gaci.
Furta ra’ayi kuma bisa doron mulkin dimukuradiyya abu ne da kowa ke da dama gwargwadon yadda doka ta tanada. Saboda haka ya na da damar furta albarkacin bakinsa. Kuma ya na da damar ya tsuke bakinsa, ya yi kurum.
‘Yan Sanda Sun Ceto Ɗaliban Makarantar Lauyoyi Guda Shida Da Aka Yi Garkuwa Da Su
Na hangi wani ra’ayin sa kan yadda za a samu nasara a Kano idan shekerar zabe ta 2027 ta zo, a wasu daga cikin kafafen yada labarai a nan jihar Kano. Kuma har kawo zuwa yanzu ban ji an ce ya fito ya karyata abinda a ka ce ya fada ba.
Babban abinda ra’ayinsa ke nunawa shine, in dai maganar takarar gwamna a ke a shekarar zabe ta 2027 a Kano, to ba wanda ya fi kowa cancanta sama da Mataimakin Shugaban Majalisar Dattawa na Kasa, Sanata Barau Jibrin.
Sa’annan kuma tsohon gwamnan jihar Kano kuma tsohon dan takarar gwamna na APC a 2023, Nasiru Yusuf Gawuna da kuma tsohon dan takarar mataimakin gwamna Murtala Sule Garo, su kuma abinda ya fi cancanta gare su shine, su fito takarar Sanatoci daga Kano ta Tsakiya da kuma Kano ta Arewa. Wannan shine ra’ayin Minista.
Ni dai abu na farko shine, ba zan ce Minista ya kwafsa ba. Amman abinda zan ce a wannan gabar shine ya kamata a ce Ministan nan ya kara fadada bayanin sa dan a samu cikakken hoton yadda abubuwan ke tafiya. Musamman a daidai lokacin da ita wannan jam’iyya ta APC ke da bukatar hada karfi fiye da yadda abin yake a da.
Na ji dadi matuka da gaske yadda shi Minista da kan sa ya ce ya san a halin da a ke ciki, ba fa wani rashin jituwa tsakanin Barau da Garo. Wannan maganar kawai abar so da alfahari ce. Kuma a kyakkyawan tsammani na ya furta wannan magana ne da sahihiyar niyya.
Na yarda Sanata Barau zai iya yin gwamnan Kano. Domin kuwa ya na da abubuwan da a ke bukata ga mutumin da zai rike irin wannan babban mukami.
Amman abin shine Minista Ata, ni a gani na, bai kara tsayawa tsaf ya kara kallon wasu damarmaki daga daya gefen ba, wadanda Sanata Barau zai fi cancantar yin su. Kuma zai yi duk abinda a ke so a wajen.
Idan mai karatu bai manta ba, a wani daga cikin rubuce – rubuce na da na yi kwanan nan, na bayyana cewar da Barau da Gawuna da Garo, dukkansu kowanne ya na da karfin siyasar da zai iya banke mulkin ‘yan koyo na jam’iyyar NNPP a Kano. Na ce wadannan mutanen guda uku duk na yarda za su iya wannan harka.
To yanzu kuma bari ma na kara da cewa, idan ba wadannan mutanen guda uku ba har yanzu, ni dai a waje na, ban ga wani wanda zai iya fizgowa ta can wani wajen da ba a tsammani ba, ya buge kowa ya tsaya wannan takara har kuma kawai a ga ya dare kan kujerar gwamna ba. Har yanzu ni dai Allah nai nuna min wannan ba.
Idan mu ka dawo kan maganar Minista ta takarar Barau a 2027,zan iya cewa ita dai wannan magana ta fito fes. Amman sai dai wani hanzari ba gudu ba, sai na ga kamar an ma manta da cewar shi fa Sanata Barau yanzu maganar matakin tarayya a ke ba jiha ba. Wannan abu ne wanda kowa ya sani. Ko mutum ya yarda ko ya watsar.
Wani abu kuma da nake kara jan hankali a kai shine, da farko dai ya danganta da yadda jam’iyyar APC ta tsara yadda za ta fuskanci zaben 2027, ina ga za a iya dauko dan takarar mataimakin shugaban kasa daga bangaren yan kabilar Igbo.
Yin hakan zai sa a dawo da shugabancin majalisar Dattawa zuwa ga Arewa. Idan kuwa hakan ta faru, kenan za a iya shiryawa Barau hanya dodar ya samu shugabancin ita majalisar ta Dattawa. Lokaci ne kawai da yadda a ka tsara abubuwan za su nuna menene abin yi idan lokacin an zo wajen.
Da zarar kuwa a ka ba bangaren Igbo takarar mataimakin shugaban kasa, to tabbas kuwa zai canza lissafin yan kabilar Igbo din ga maganar neman shugabancin kasa. Za su ga an kara matsar da su kusa – kusa da mulkin kasa. Kuma a hangen su, ta hanya mafi sauki.
Tabbataccen abu shine, babu ta yadda za a yi yan kabilar Igbo su kadai ba tare da hada gwuiwa da wasu kabilun ba, a ce za su iya samun shugabancin kasar nan. Haka abin yake ma a wajen ragowar kabilun kasar nan. Babu wanda ya isa ya rayu shi kadai tilo ba tare da kama – kama ba.
Ina ga zai fi kyau da a ce Minista Ata ya kara fadada ra’ayinsa da zai hango cewar, ai kuwa Sanata Barau ya ma kamata a daga likkafarsa zuwa wani mataki na gaba. Kamar ma mukamin mataimakin shugaban kasa. Duk abu ne mai yiwuwa. Musamman mu da mu ka san Allah ne ke yi. Ba wani ba, ba kuma wata dabara ba.
Abubuwan dai duka sun danganta ne da yadda a ka tsara yadda za a yi tafiyar ta 2027 din. Tare da kuma yadda a ka kokarta wajen ganin an samu daidaiton fahimta da alkiblantar nahiya daya tsakanin manyan jam’iyyar ta APC masu amfani. Hakan kadai shine zai kawo cigaba da samun nasara a tafiyar.
Yanzu misali idan ka duba zaben 2023 da a ka yi na shugaban kasa, Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya samu kuri’u 517,341 a Kano. Yayin da jihar Barno ta ba shi kuri’u 252, 282. Kamar dai yadda hukumar zabe mai zaman kan ta ta kasa ta bayyana. Ka ga kuri’un Kano sun nunka na Barno har da doriya.
Shiyyar Arewa Maso Yamma ta ba Tinubu kuri’u 2,652,235. Yayin da shiyyar Arewa Maso Gabas, wacce jihar Barno ke wajen tare da dan takarar mataimakin shugaban kasa na lokacin yake, wato Kashim Shettima, kuri’u 1,185,458. Wanda ko rabin abinda Arewa Maso Yamma ta bayar bai kai ba.
Wato ina yin wannan magana ne saboda na mayar da martani ga masu cewar wai idan Tinubu ya ki tafiya da Shettima a zaben 2027, APC za ta yi gagarumar asarar kuri’u daga Barno da kuma ma wai shiyyar Arewa Maso Gabas gaba daya.
An manta da cewar a shiyyar ba fa yan gidan mutum daya ba ne su gaba dayansu. To kuma ma da kuri’un shiyyar Arewa Maso Yamma da kuma na shiyyar Arewa Maso Gabas wadanne ne ya kamata shugaba Tinubu ya ririta? Ba fa wai a na cewa an shirya da asarar kuri’un ko ina ba ne fa. Kawai dai ina bayar da yadda lissafin alkaluman suke ne.
Wani abin lura din kuma shine, a Arewa Maso Yamma akwai jihohi guda 7. Yayin da a Arewa Maso Gabas kuma suke da jihohi guda 6. To ba ma wannan ba, kuri’un da jihar Kano ta ba wa Tinubu a 2023, sun fi kuri’un da jihohi 3 na shiyyar Arewa Maso Gabas su ka ba shi.
Misali Kano ta ba shi kuri’u 517,341. Yayin da jihar Gombe ta ba shi kuri’u 146,977. Jihar Taraba ta ba shi kuri’u 135,165. Yayin da jihar Yobe ta ba shi kuri’u 151,459. Ka ga kuwa lallai banbancin a bayyane yake firi-falo.
Wani babban abin ban sha’awa kuma shine, hukumar nan ta raya bangaren Arewa Maso Yamma ( wato North West Development Commission) da Tinubu ya kirkira za ta taimaka masa wajen samun kuri’unsa a kakar zabe ta 2027. Ba ma nan ba kawai, hatta irin kokarin da Sanata Barau ya yi wajen kafa hukumar har yanzu jama’ar wannan shiyya ba su manta da wannan babban abin alherin ba.
Bayan wasu abubuwan raya kasa da raya al’umma da Sanatan ya kawo musu. Kamar kuma yadda dabi’ar mutane take, da yawa sun kuduri aniyar saka masa da alheri duk lokacin da bukatar hakan ta taso. Mutane da yawa da mu ka tattauna da su a wani binciken mu, sun nuna mana cewa su fa kawai so suke lokacin da Barau zai bukace su, dan ya ga halacci. Kenan ka ga Barau ashe wata kadara ce a hannun Tinubu idan ya fahimci hakan. Shi Tinubun kenan.
Wani babban abin lura dai a nan shine, muddin Tinubu zai iya sasanta tsakanin jagororin APC a jihar Kano, wajen sa wa su fuskanci alkibla daya yayin neman kuri’un al’umma da kuma dukkanin al’amura na jam’iyyar, to kuwa zai iya kare kuri’un da a ka ba shi a jihar tare da watakila ma ya kara samun wasu a kan na da din. Musamman, musamman ma dai idan a ka kara saukakawa talaka rayuwa.
Duka duka dai abubuwan gaba daya sun ta’allaka ne kan yadda a ka shiryawa harkar. Tabbas abinda Minista Ata ya fada akwai dalilin sa mai karfi da ya sa ya fadi hakan. Amman dai ya kamata ya lura da cewar, har yau har gobe, tikitin takarar Gawuna – Garo ya na fa da tagomashi a Kano.
Haka nan za ma a iya juya abin ya zama Garo – Gawuna. Shi ma hakan tabbas zai iya samun tagomashi. Tsakanin Gawuna da Garo, kowannensu na bukatar kowa. Kuma Barau ya na bukatar su gaba daya.
Kafin dai na manta bari na yi bayanin cewa, na san wasu abubuwa da a ke yi ta karkashin kasa, na sasanta jiga-jigan tafiyar nan dan cigaban jam’iyyar. Wasu abubuwan kuma kishin-kishin din su nake ji. Amman kuma tabbas akwai su a na yi.
Misali yanzu tsakanin Barau da Garo an fara samun fahimtar juna. Ba kamar yadda a da wasu masu zaman cin amana suke ta shige – da-fice ba tsakanin jagorori.
Kowa ya san irin yadda tsohon gwamnan jihar Kano Dr Abdullahi Umar Ganduje CON, a matsayin sa na uba ya yi ta kokarin sasanta wasu daga cikin jigogin tafiyar. Har sai da ta kai an sa Garo ya zama babban daraktan kamfen na neman kujerar Sanata da Barau ya yi a can baya. Da kuma yadda shi kan sa Ganduje ya soke tasa takarar ta Sanata ya sakarwa Barau.
Tun daga lokacin sai wasu masu kishin jam’iyyar su ka cigaba da irin wancan kokarin sasantawar. A nan ba zan manta da mutane irin su tsohon mai ba wa gwamna shawara kan wayar da kan ka al’umma tun daga tushe, wato Yusuf Aliyu Tumfafi, kan irin yadda yake kai gwauro ya kai mari na samun daidaito tsakanin jagorori ba. Wanda na tabbatar duk lokacin da ya samu dama zai iya harhado kan yan jam’iyya dan samun zartacciyar nasara da cigaban al’umma.
Ina mai kara tabbatar wa da mai karatu cewar, in dai Tinubun da na sani ne a can baya, tun lokacin mulkin soja, a lokacin ina tare da kungiyar sa kai ta wani babban lauya Dr Tunji Abayomi, wato “Nigerianity Movement” daga baya kuma “Human Rights Africa” yadda mu ka karu da dabarun samun nasara wajen yakar bakin mulkin soja a lokacin, tun wajejen 1998, daga irin ayyuka da shawarwari ga yan gwagwarmaya, to kuwa na tabbatar Tinubu ba zai wofantar da Kano ba.
Ya san wadanne irin dabaru zai amfani da su wajen lalubo bakin zaren. Wannan, in dai yadda na san shi a da har yanzu haka yake, to kuwa yan adawa za su sha mamaki. Ba na raba daya biyu.
Kamar kuma yadda watakila zan iya yarda da abinda Minista Ata ya ce, duk da haka ina fatan kara bude hange da kuma hasashe kan makomar Sanata Barau. Abin dai gaba daya ya ma ta’allaka ne kan ta gefen da mutum mai nazari ke kallon al’amuran.
Sa’annan kuma wani babban abinda nake da sha’awa a kai shine, ya kamata dai shugaba Tinubu ya san da cewa da Gawuna da Garo fa har yanzu su na nan a raye kuma har gobe su na da irin tasu hobbasar.
Saboda haka matso da su kusa da mulki zai iya canza wasu abubuwa. A can baya dai mun ga yadda a ke ta yi wa Barau sharrin cewa shine kanwa uwar gamin hana Gawuna da Garo matsawa kusa kusa. Amman ai daga baya an ga yadda gizo yake sakar. Wannan ba kuma boyayyen abu ba ne yanzu. Amma fa ga mai tsinkaye.
Sannan kuma ya kamata Tinubun dai ya kara fahimtar waye Barau da irin yadda yake wajen kokari da jajircewa. Ya kamata dai shugaban kasa ya kara fahimtar Barau da kyau da gaske. Hakan zai taimaki shugaban kasa gaya.
Ni dai yadda nake ganin yadda al’amura ke gudana, ban fitar da rai ba cewar Barau zai iya zama mataimakin shugaban kasa ko kuma shugaban majalisar dattawa na kasa. Ko kuma ma dai wani abinda Allah Ya zaba masa shugaba Tinubu zai aiwatar.
Anwar ya yi wannan rubutu ne daga Kano
Asabar, 2 ga Agusta, 2027
