Connect with us

News

SKY Ya Bukaci Gwamnati Ta Mayar Da Hankali Kan Rage Talauci A tsakanin Al’umma

Published

on

IMG 20250731 WA0000

Fitaccen ɗan kasuwa daga jihar Kano, Alhaji Kabiru Sani Kwangila Yakasai (SKY), ya bukaci gwamnatocin ƙasa da na jihohi da su mai da hankali wajen gudanar da ayyuka masu tasiri kai tsaye a rayuwar al’umma, domin rage radadin talauci da matsin rayuwa da ke addabar jama’a.

Alhaji SKY ya bayyana hakan ne a yayin bikin rufe karatun littafin Ashfa, wanda Malam Abdulkadir Shehu Mai Anwar ya gabatar a unguwar Tudun Yola da ke ƙaramar hukumar Gwale a jihar Kano.

Advertisement

Shugaba Tinubu ya tsawaita wa’adin shugaban kwastam na Najeriya

Ya ce, bayan shekaru biyu da gwamnoni suka kwashe suna gudanar da manyan ayyuka, lokaci ya yi da za su karkata zuwa kananan ayyuka da za su iya shafar rayuwar talakawa kai tsaye – kamar ayyukan taimakon sana’o’i, gine-gine, da tsare-tsaren da za su rage laifuka a cikin al’umma.

“Al’umma suna cikin wani hali na matsin tattalin arziki da talauci. Gwamnati ta dace ta duba hanyoyin da za su sauƙaƙa musu rayuwa, musamman ta hanyar samar da ayyukan yi da kuma tallafin sana’o’i,” in ji SKY.

Advertisement

Ya kuma yi kira ga gwamnoni da su ware kudade na musamman domin tallafa wa ƴan kasuwa da masu sana’o’in hannu, musamman a wannan lokaci da yawa daga cikinsu suka yi asarar jari saboda hauhawar farashi da tsadar kasuwanci.

SKY ya jaddada bukatar gwamnati, musamman ta Tarayya da ta jihohin Arewa, da su fito da hanyoyin da za su tallafa wa jama’a wajen rage fatara, da inganta zaman lafiya a cikin al’umma.

Advertisement

Haka kuma, ya shawarci gwamnatocin jihohi da su samar da takin noma kyauta ga manoma, yana mai cewa tsadar taki a yanzu na barazana ga kokarin gwamnati na tabbatar da wadataccen abinci mai saukin farashi.

A cewarsa, samar da gidajen saukin kudi a cikin manyan birane ma na daga cikin matakan da za su rage cinkoso da kuma aikata laifuka a tsakanin matasa.

Advertisement

Taron ya samu halartar fitattun mutane daga sassa daban-daban na ƙasa, ciki har da limamai, da Hakimin Kaura Namoda daga jihar Zamfara, da sauran manyan baki.

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending