Connect with us

News

Ba Mu Da Hannu A Rahoton Sukar Gwamnatin Kano — Cewar Ƙungiyoyin Masu Buƙata Ta Musamman

Published

on

Ƙungiyoyin haɗin gwiwa na mutane masu buƙata ta musamman a jihar Kano sun nesanta kansu daga wani rahoto da aka wallafa a wani shafin intanet, wanda ya nuna cewa sun soki gwamnatin jihar kan jinkirin kafa hukumar kula da su.

A wata sanarwa da suka fitar a ranar Alhamis, mai ɗauke da sa hannun Abdulrahman Uba Daushe, shugaban ƙungiyar masu raunin kashin baya a jihar, ƙungiyoyin sun ce rahoton ya yi ƙarya da yaudara.

Advertisement

Shugaba Tinubu ya tsawaita wa’adin shugaban kwastam na Najeriya

Rahoton da aka wallafa a Jaridar Internet a ranar 30 ga Yuli, 2025, ya nuna cewa kungiyoyin sun bayyana rashin jin daɗinsu game da yadda gwamnatin ke tafiyar da batun kafa hukumar kula da masu buƙata ta musamman.

Sai dai sanarwar ta ƙaryata hakan tana mai cewa:l “Ba mu halarci wani taro da ya shafi wannan batun ba, kuma ba mu fitar da wata sanarwa ko sukar gwamnati ba.”

Advertisement

Ƙungiyoyin sun bayyana cewa hoton da aka saka a rahoton ya fito ne daga wani taro daban da aka gudanar a ranar 22 ga Yuli, mai taken: “Tattaunawa da masu ruwa da tsaki kan tallafawa mutane masu buƙata ta musamman a Kano.”

Sun ƙara da cewa wani daga cikin shugabanninsu ya halarci taron, amma a matsayin kansa, ba a madadin ƙungiyoyin ba.

Advertisement

Bayan rahoton ya fito, ƙungiyoyin sun ce sun tuntubi masu shirya taron da wasu daga cikin mahalarta, inda suka bayyana mamaki kan yadda aka fassara abubuwan da suka faru.

“A duk lokacin da muka miƙa buƙatun da suka shafi walwalar mutane masu buƙata ta musamman, gwamnati ba ta taɓa ƙin amincewa da su ba,” in ji sanarwar.

Advertisement

Kungiyoyin sun kuma ja hankalin sauran masu fafutuka da su guji yada bayanan da ba su da tushe, tare da neman a ci gaba da tattaunawa da fahimtar juna tsakanin kungiyoyi da gwamnati.

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending