Connect with us

News

Shugaba Tinubu ya tsawaita wa’adin shugaban kwastam na Najeriya

Published

on

FB IMG 1753966937986

Shugaban Najeriya Bola Tinubu ya amince da tsawaita wa’adin shugaban hukumar kwastam ta ƙasar, Bashir Adeniyi.

Cikin wata sanarwar da fadar shugaban ƙasar ta fitar ta ce Tinubu ya tsawaita wa’adin Adeniyi – wanda zai ƙare ranar 31 ga watan Agusta mai zuwa – da shekara guda.

Al’umar Ghana Na Zanga-zangar Korar ‘Yan Najeriya Daga Ƙasar

Sanarwar ta ce tsawaita wa’adin zai bai wa Adeniyi damar ƙarasa aiwatar da sauye-sauye masu muhimmanci da hukumar ke gudanarwa ƙarƙashin mulkin Tinubu.

“Shugaban ƙasa na da ƙwarin gwiwar tsawaita wa’adin zai ƙarfafa ayyukan hukumar wajen tsara manufofin kasuwanci da karɓar haraji da tabbatar da tsaron kan iyakoki”, in ji sanarwar.

A watan Octoban 2023 ne Tinubu ya naɗa Adeniyi a matsayin shugaban hukumar kwastam ta Najeriya.

Kafin nan ya riƙe mukamin a matsayin shugaban riƙo bayan saukar tsohon shugaban hukumar Hameed Ali.

Advertisement

 

 

BBC HAUSA

Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending