News
Al’umar Ghana Na Zanga-zangar Korar ‘Yan Najeriya Daga Ƙasar
Wasu al’ummomin Ghana sun fito zanga-zanga a babban birnin kasar, Accra, domin nuna ƙin amincewarsu da zaman ’yan Najeriya a ƙasarsu, bisa zargin aikata laifuka da kuma karya dokokin kasuwanci.
Masu zanga-zangar dai sun mamaye wasu manyan tituna da kasuwanni, musamman kasuwar Circle da ke Accra – inda ake ganin cunkoson ’yan Najeriya da ke gudanar da harkokin kasuwanci iri-iri.
Sojojin Najeriya Sun Kashe Ƴan Ta’adda 3,000, Fiye Da 12,000 Sun Miƙa Wuya A Shekaru Biyu
Sun zargi ’yan Najeriya da aikata laifukan kisan kai da kuma harkar karuwanci, tare da mamaye kasuwannin da kamata ya yi ’yan asalin kasar su fi cin gajiyarsu.
A cewar masu zanga-zangar, hakan na kara tabarbarewar tattalin arziki da hana ’yan Ghana samun abinci a bakinsu.
“Ya zama dole gwamnati ta dauki mataki, ba za mu ci gaba da zuba ido ana ci mana tuwo a kwarya ba,” in ji wani daga cikin shugabannin zanga-zangar da ke jawabi ga FRI HAUSA.
Rahotanni na nuni da cewa an kara yawan jami’an tsaro a kasuwar Circle domin shawo kan duk wata tarzoma, yayinda ’yan Najeriya da ke kasuwanci a wurin ke gudanar da ayyukansu cikin fargaba.
Wani dan kasuwa daga Najeriya da ya bukaci a sakaya sunansa ya ce, “Muna gudanar da kasuwanci ne bisa doka, amma ana mana kallon da bai dace ba. Muna rokon gwamnati ta karemu.”
Wasu masu sharhi na ganin cewa wannan zanga-zangar na da nasaba da matsin tattalin arziki da ke addabar kasashen yankin, wanda ke haifar da gasa tsakanin ’yan kasa da baki wajen samun damar rayuwa.
