News
Gudanar Da Dukkan Zaɓuka A Rana Ɗaya Abu Ne Wanda Zai Haifar Da Rudani —Jami’in INEC
Wani jami’i a Hukumar Zaɓe Mai Zaman Kanta ta Ƙasa (INEC) ya bayyana cewa ƙudirin Majalisar Tarayya na gudanar da dukkan manyan zaɓuɓɓuka a rana ɗaya ba zai yiwu ba, tare da jan hankalin ‘yan majalisa da su soke wannan ƙudiri.
Jami’in, wanda ya buƙaci a ɓoye sunansa, ya bayyana hakan ne cikin wata hira da Kamfanin Dillancin Labarai na Najeriya (NAN) a Abuja, ranar Alhamis.
Sanata Barau, Laluben Ruhin APC a Arewa da Manufofin Al’umma
A cewar sa, aiwatar da zaɓen shugaban ƙasa, gwamnoni, ‘yan majalisar dattawa, ‘yan majalisar wakilai da kuma na majalisun dokoki na jihohi a rana guda, ba zai iya tafiya cikin sahihanci da tsari mai kyau ba.
Ya ce, “Ba wai INEC ba ta da ƙwarewa ba ne, amma tsarin ya fi ƙarfin aiwatarwa bisa yanayin dabaru da kayan aiki da ake da su a yanzu.”
Ya ƙara da cewa kundin tsarin mulki ya bai wa INEC cikakken ‘yanci da ikon zaɓar ranakun gudanar da zaɓe, don haka ya kamata ‘yan majalisar kada su kawo dokar da za ta tauye wannan iko.
A makon da ya gabata ne Majalisar Wakilai ta tsallaka karatu na biyu a kan wani kudiri da ke neman sauya tsarin gudanar da zaɓe a Najeriya, ta hanyar gudanar da dukkan zaɓuka a rana ɗaya daga shekarar 2027.
Haka kuma, NAN ta ruwaito cewa ƙungiyar dattawan ƙasa ta The Patriots ƙarƙashin jagorancin tsohon Sakataren Ƙungiyar Commonwealth, Cif Emeka Anyaoku, ta yi kiran a sauya tsarin zaɓe, a wani babban taro da aka shirya kan makomar kundin tsarin mulki da dimokuraɗiyya a Najeriya.
Sai dai INEC na ganin cewa cunkuson ayyuka a rana ɗaya na iya haifar da rikice-rikice, rage yawan jami’an da za su iya gudanar da zaɓen yadda ya kamata, da kuma ƙalubale wajen tantance sakamakon zaɓe cikin lokaci.
“Zaɓe a rana guda tamkar juyin juya hali ne ga tsarinmu, kuma zai buƙaci ƙarin ƙarfi da albarkatu da ba su samuwa a halin yanzu,” in ji jami’in.
