News
Martani Kan – Ziyarar Tinubu a Kano: Shaidar Ƙarfin Siyasar Sanata Barau a Arewacin Najeriya
DAGA ABBA ANWAR, KANO
Ziyarar da Shugaban Ƙasa, Bola Ahmed Tinubu, ya kai Jihar Kano a makon da ya gabata, ta sake fayyace irin tasiri da ƙarfafa matsayin Sanata Barau I. Jibrin, mataimakin shugaban Majalisar Dattawa, a siyasar Arewacin Najeriya baki ɗaya, ba kawai a jihar Kano ba.
A wani rubutu da Alhaji Fahad Ogan Boye ya wallafa a jaridar Daily Trust a ranar Asabar, 19 ga Yuli, an bayyana wannan ziyarar a matsayin alamar girmamawa da daraja da ake wa Sanata Barau a duniyar siyasa. A cewarsa, Sanatan ya zama ginshiƙi mai ƙarfi a jam’iyyar APC a Arewa, wanda ke da tasiri mai zurfi wajen tsara makomar siyasa a yankin.
Barau Ikon Allah: Siyasar Da Aka Gina A Kan Haƙuri Da Hikima
Sai dai a nawa dan karamin nazarin harkokin siyasa, ina ganin cewa wannan rubutu bai isar da cikakken bayani game da hakikanin rawar da Sanatan ke takawa ba. Musamman wajen kafa tubalin da ya share masa fagen samun wannan matsayi na daraja da karbuwa.
Babban abin lura kuwa wanda marubucin bai fada ba shine, biyayya ga shugabanci da manya na gaba, shine daya daga cikin ginshikan da su ka ba Sanata Barau ire-iren wadannan darajoji. Kai dai da gani ba tambaya.
Ya na da kyau idan a ka kara da cewa irin biyayyar ban girma da Sanatan ke wa shugaba Tinubu, ita ma wata ginshikin abu ce da take kara fito da dattako da girmama dan Adam da a ka san Barau da shi.
Sanata Barau, wanda aka sani da jajircewarsa da kishin al’umma, ya dade yana taka muhimmiyar rawa wajen inganta rayuwar al’umma ta hanyar bayar da tallafi, shirye-shiryen ilimi ga matasa, da kuma ƙarfafa tsarin shugabanci nagari.
Ya kasance daga cikin shahararrun masu goyon bayan Shugaba Tinubu tun kafin hawansa kan madafun iko, tare da kasancewa ɗaya daga cikin ‘yan majalisar da su ka fi kwarewa da cika alƙawura. Ya kamata a fito da irin wadannan abubuwan. Saboda muhimmancin su.
Gaskiya ne kuma kamar yadda marubucin ya ce “Daga cikin manyan abubuwan da suka jawo masa yabo, har da ƙudurin kafa Hukumar Raya Arewa masu Yamma (North West Development Commission) – wani muhimmin tsari da ke da nufin inganta ci gaban yankin da rage gibin cigaba tsakanin Arewa da sauran sassan ƙasa.”
Haka yake kuma ina ganin cewa ayyukan Sanatan sun wuce jihar Kano, domin kuwa ya gabatar da muhimman kudurori da suka shafi ci gaban ƙasa baki ɗaya – musamman a fannonin ilimi, lafiya da walwalar al’umma.
Ya kuma kamata shi wannan marubuci ya gane cewar Sanata Barau na da karɓuwa a tsakanin kowane ɓangare na al’umma, ba tare da nuna bambanci ba – abin da ke ƙara masa daraja a idon jama’a. Wannan ne ya ba shi damar zama First Deputy Speaker a Majalisar ECOWAS, wani matsayi da ke ƙara nuna yadda aka amince da ƙwarewarsa a matakin ƙasa da ƙasa.
Rubutun Ogan Boye ya ce: “Sanata Barau mutum ne mai kwazo da hangen nesa. Ya shahara wajen gabatar da muhimman kudurori da suka shafi ci gaban jama’a, tare da kyakkyawar mu’amala da takwarorinsa a Majalisar Dattawa.”
Wasu masana siyasa na ganin cewa tare da irin wannan karbuwa da goyon baya da Sanata Barau ke da shi a Arewacin Najeriya, zai taka muhimmiyar rawa wajen tallafawa Shugaba Tinubu da jam’iyyar APC domin samun gagarumar nasara a babban zaɓen 2027.
Kuma ya kamata marubucin ya fito da maganar cewa Sanatoci da dama sun yaba masa da dattaku, gaskiya, da jajircewa a harkar majalisa – halaye da ke ƙara masa karɓuwa a ciki da wajen majalisa.
Wannan kuwa shi ne irin jagorancin da Arewacin Najeriya ke buƙata: wanda ke sauraron jama’a, yana aiki tare da su, kuma yana da sauƙin kai. A cewar wasu masu fashin baki, hakan na nuni da cewa Sanata Barau yana daga cikin amintattun shugabannin da Shugaba Tinubu ya kamata ya ci gaba da dogaro da su, musamman wajen ƙarfafa jam’iyyar APC a Arewa.
