Connect with us

News

‎Kwamishina A Kano Ya Yi Belin Mutumin Da Ake Zargi Da Safarar Miyagun Kwayoyi Sulaiman Danwawu ‎

Published

on

1753396125570

Kwamishinan Sifiri na jihar Kano Ibrahim Namadi ya yi belin Sulaiman Danwawu mutumin da ake zargin sa da kasancewa kasurgumin dilar miyagun kwayoyi ne.

‎Jaridar DAILY NIGERIAN ta ruwaito cewa tun farko alkalin kotu ya sanya kaidoji masu tsauri kafin ya ba da belin Danwawu, inda ya ce in yana bukatar a sake shi sai ya kawo wani mutum da zai tsaya masa kuma Kwamishina jihar Kano da kuma kudi Naira miliyan 5.

Advertisement

Yadda shirin ‘Safe Corridor’ ke sauya rayuwar matasan da suka taɓa fadawa cikin harkar ta’addanci da shaye-shaye a Kano

‎Rahoton ya ce Namadi ya cika wannan sharadi, inda ya rubuta takarda zuwa ga Mataimakin Babban Sakataren Shari’a na kotun, yana bayyana aniyarsa ta tsayawa Danwawu.

‎Cikin takardar da aka aike a ranar 18 ga Yuli, 2025, kwamishinan ya bayyana cewa:

Advertisement

‎ “Ina rokon kotu da ta amince da bukatata ta tsayawa wanda ake tuhuma (Sulaiman Aminu) bisa belinsa akan sharuddan da aka gindaya.”

‎“Na kuma dauki alhakin cika dukkan sharuddan da kotu ta shimfida, da kuma tabbatar da cewa wanda ake tuhuma zai halarci duk wani zaman kotu har zuwa karshe,” in ji Namadi.

Advertisement

‎Sai dai har zuwa lokacin da ake kammala wannan rahoto, kokarin da aka yi na jin ta bakin Kwamishinan bai kai ga nasara ba, domin ya ce yana cikin taro, kuma bai dawo da kira ba daga baya.

‎A ranar 21 ga Mayu, hukumar hana sha da fataucin miyagun kwayoyi ta kasa (NDLEA) ta shigar da tuhuma takwas kan Danwawu a gaban kotun tarayya da ke Kano.

Advertisement

‎An gurfanar da shi a ranar 28 ga watan Mayu, inda kotu ta tura shi gidan yari, kafin daga bisani a amince da bukatar belinsa.

‎Lamarin dai ya jawo ce-ce-ku-ce a tsakanin al’umma, duba da matsayin wanda ya tsaya masa da kuma nauyin zargin da ke kansa.

Advertisement

‎Kungiyar Lauyoyi ta Najeriya reshen Kano (NBA) ta bayyana cewa za ta sanya ido sosai kan yadda shari’ar ke gudana, duba da muhimmancinta ga walwalar jama’a da tsarin adalci.

 

Advertisement

 

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending