News
Yadda shirin ‘Safe Corridor’ ke sauya rayuwar matasan da suka taɓa fadawa cikin harkar ta’addanci da shaye-shaye a Kano
Kwamishinan Yaɗa Labarai da Harkokin Cikin Gida na Jihar Kano, Kwamared Ibrahim Abdullahi Waiya, ya bayyana cewa shirin ‘Safe Corridor: The Kano Model’ da gwamnatin jihar ke aiwatarwa ya fara haifar da gagarumar nasara wajen sauya tunanin matasa da suka taɓa fadawa cikin harkar ta’addanci da shaye-shaye.
Kwamishina Waiya ya bayyana haka ne a lokacin da mai jagorantar Cibiyar Gyaran Halaye ta Kiru, Ms. Cheryl Aminta Kwagga, ta kai masa ziyara a ofishinsa domin neman haɗin gwiwa a ƙoƙarin da cibiyar ke yi na farfaɗo da rayuwar matasa da suka faɗa cikin mugayen dabi’u.
“Mun samu matasa da dama da suka bayyana aniyar barin harkar ta’addanci da shaye-shaye, suna kuma shirye-shiryen zama masu amfani ga kansu da al’umma. Wannan alama ce ta nasarar da shirin ‘Safe Corridor’ ya fara samu,” in ji Kwamishinan.
Ya ƙara da cewa gwamnatin jihar ta tsara shirin ne domin janyo matasa da ke kan hanya mara kyau su tuba, sannan a tallafa musu ta hanyar horo, gyaran hali da ƙarfafa masu gwiwa, domin sake gina rayuwarsu.
Kwamishinan ya bayyana cewa Ma’aikatar da yake jagoranta za ta haɗa kai da Cibiyar Kiru wajen shirya tarurrukan wayar da kai da kuma isar da saƙonni zuwa ga jama’a, musamman iyaye da matasa, domin fahimtar illolin da ke tattare da shaye-shaye da ta’addanci.
A nata jawabin, Ms. Cheryl Aminta Kwagga ta yaba da irin goyon bayan da Ma’aikatar ke bayarwa, tana mai cewa akwai buƙatar haɗin gwiwar hukumomi da ƙungiyoyin farar hula domin ceton rayuwar matasa.
“Wannan yaƙi ba namu ne kaɗai ba. Muna buƙatar haɗin gwiwa da hukumomi masu tasiri kamar Ma’aikatar Labarai domin samun sauyi mai ɗorewa a cikin al’umma,” in ji Ms. Kwagga.
