Politics
Yadda Ganduje Ya Maida Hankali Wajen Gina Jam’iyyar APC Don Tunkarar Zaben 2027

DAGA UMAR IDRIS SHUAIBU, KANO
A yadda siyasa ta kamata ta kasance, shugabanci bai takaita ga samun madafun iko ba, illa ya kasance hanyar ciyar da kasa gaba, karfafa al’umma da gina tubalin ci gaba mai dorewa.
Tun bayan nada Dakta Abdullahi Umar Ganduje a matsayin Shugaban Jam’iyyar APC na kasa a watan Agustan 2023, ya mayar da hankali kan sasanta rikice-rikicen bayan zabe da kuma hada kan ‘ya’yan jam’iyya don kara karfafa ta a fadin kasa.
Abba Anwar Ya Kare Ganduje: “Ganduje Jagoran Zaman Lafiya Ne, Ba Mai Son Rikici Ba!”
Wannan mataki ya zo a lokacin da aka fuskanci baraka a sassa daban-daban na kasa sakamakon sakamakon zaben 2023, inda Ganduje ya taka muhimmiyar rawa wajen warware sabani da gina zaman lafiya a cikin jam’iyyar. Hakan ya taimaka wajen rage yawan sauya sheka da ake fuskanta a siyasance.
Dakta Ganduje ya karfafa martabar jam’iyyar APC ta hanyar bude kofar tattaunawa da sauraron matsalolin ‘ya’yan jam’iyya tare da samar da tsarin da ya ba kowa damar shiga da bayyana ra’ayinsa.
A karkashin shugabancinsa, jam’iyyar ta guji tsarin danniya da son zuciya wajen fitar da ‘yan takara. A maimakon haka, an bullo da tsari na tattaunawa da jituwa tsakanin ‘yan takara don fitar da wanda ya fi cancanta, tare da karfafa mata da matasa a harkokin jam’iyya.
Daga cikin muhimman sauye-sauyen da Ganduje ya kawo akwai:
Bai wa ‘yan takara damar sulhu da fitar da wanda suka yarda da shi.
Karfafa gwiwar mata da matasa a harkokin siyasa da shugabanci.
Zartas da matakai bisa hujjoji da a fili.
Wadannan matakai sun kara tabbatar da daraja da mutuncin jam’iyyar mai mulki a idon jama’a.
Haka zalika, Ganduje ya kara fadada tasirin jam’iyyar APC zuwa yankunan da ba ta da karfi a da, musamman Kudu maso Gabas da Kudu maso Kudu. Wannan ya kasance ne sakamakon tuntuba da kokarin samar da fahimta da hadin kai a wadannan yankuna, lamarin da ke nuna yiwuwar jam’iyyar ta samu nasara a wadannan yankuna a zaben 2027.
A gefe guda kuma, Ganduje ya bijiro da sabbin hanyoyin gudanar da ayyukan jam’iyya ta hanyar amfani da fasahar zamani. Ciki har da:
RAJISTAR ‘YAN JAM’IYYA TA INTANET
Biyan kudaden jam’iyya ta kafar zamani
Amfani da shafukan sada zumunta wajen yada ayyukan jam’iyya da tallata manufofinta
Wadannan sauye-sauye sun kara wa jam’iyyar kuzari da karfi wajen fuskantar kalubalen zabe a nan gaba.
Ganduje ya kuma yi kokari wajen dawo da wasu fitattun ‘yan siyasa cikin jam’iyyar, matakin da ke rage karfin ‘yan hamayya tare da karfafa gwamnatin mai ci.
A karshe, shugabancin Dakta Abdullahi Umar Ganduje na kokarin kafa tubalin da za a gina jam’iyyar APC a kai cikin karfi da hadin kai, domin samun nasara mai dorewa a zabukan 2027 da kuma bayan haka.