Connect with us

News

‎Abba Anwar Ya Kare Ganduje: “Ganduje Jagoran Zaman Lafiya Ne, Ba Mai Son Rikici Ba!” ‎

Published

on

Tsohon Sakataren Yaɗa Labarai na tsohon Gwamnan Kano, Dr Abdullahi Umar Ganduje, wato Abba Anwar, ya maida martani mai zafi kan wani rubutu da aka buga a wata jarida mai taken: “The Decoration of Ganduje As A Peace Ambassador: Unmasking A Legacy Of Divisiveness And Manipulation.”

‎A cikin martanin da ya cika da hujjoji da kwararan misalai, Anwar ya bayyana rubutun da wani Gwadabe Abdullahi daga unguwar Sanka ya wallafa a matsayin “tarin kuskure da rashin fahimta,” yana mai cewa babu wani hujja mai karfi da ta rushe hujjojin da ya gabatar a baya.

Advertisement

Kungiyar SERAP Ta Bukaci Gwamnati Ta Fara Bincike Kan Bacewar Biliyan 233 Kafin Karɓar Sabon Bashi

‎Anwar ya jaddada cewa Ganduje ya kafa tarihi wajen inganta zaman lafiya da tsaro a Kano, inda ya lissafo wasu daga cikin manyan matakan da ya ɗauka, kamar haka:

‎Gina cibiyar sa ido da leƙen asiri a Bompai;

Advertisement

‎Kafa dakunan kwana ga jami’an tsaro a manyan hanyoyin fita daga birnin Kano;

‎Sauya gandun dajin Falgore zuwa filin atisayen sojoji;

Advertisement

‎Shirya taron sulhu tsakanin shugabannin al’ummar Igbo da matasan Arewa;

‎Tattaunawa da malaman addini kafin ɗaukar mataki a lokutan rikice-rikice.

Advertisement

‎Kan zargin cewa Ganduje ya kawo rabuwar kawuna tsakanin malamai, Anwar ya ce: “Babu wani sabon majalisar malamai da aka kafa domin hamayya da Shaykh Ibrahim Khalil.” Ya ce gina masallatai ba laifi ba ne, kuma bai kamata a fassara hakan a matsayin dabara ta siyasa ba.

‎Game da sauya sunayen garuruwa da jami’a, Anwar ya kare matakin gwamnatin Ganduje na sauya sunan Jami’ar Northwest zuwa Yusuf Maitama Sule University, da kuma canza sunan Kwankwasiyya City zuwa Sheikh Khalifa Isyaka Rabi’u City. Ya ce waɗanda aka saka sunayensu manyan malamai ne da suka cancanci a girmama su.

Advertisement

‎Anwar ya jaddada cewa kowa na da ‘yancin sukar gwamnati, amma ya kamata hakan ya zama bisa hujja da gaskiya, ba jita-jita ko son zuciya ba.

‎A ƙarshe, Anwar ya bayyana cewa duk da cewa akwai masu adawa da Ganduje, tarihin ayyukansa da ƙoƙarinsa na samar da zaman lafiya a Kano ba za su goge da jita-jita ko ra’ayin wasu ba.

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending