Connect with us

News

Saudiyya Ta Karyata Sanya Takunkumin Biza Ga Najeriya Da Wasu Ƙasashe 13

Published

on

Saudiyya

Gwamnatin Saudiyya ta musanta rahotannin da ke yawo a kafafen sada zumunta da ke cewa ta sanya takunkumi ga Najeriya da wasu kasashe 13 wajen samun sabbin visa zuwa kasar.

Wasu rahotanni da suka karade Shafukan Intanet sun nuna cewa Saudiyya ta hana kasashen Najeriya, Misira, Indiya, Pakistan, Maroko, Tunisiya, Yemen, Aljeriya, Jordan, Sudan, Iraq, Indonesia, Habasha da Bangladesh neman sabbin visa na ziyarar iyali, kasuwanci, yawon bude ido, da makamantansu, tun daga ranar 13 ga Afrilu, 2025.

Advertisement

Allah ya yiwa Dr Idris Abdulazeez Dutsen Tanshi Rasuwa

A cewar takardar da ta yadu, har da gargadin cewa wanda ya karya wannan doka zai fuskanci haramcin shiga Saudiyya har na tsawon shekaru biyar.

Sai dai Jaridar THECABLE  ta ruwaito cewa Hukumar yawon bude ido ta Saudiyya ta karyata wannan takarda, tana mai cewa ba ta fito daga hukumomin kasar ba.

Advertisement

A cewarta, takardar da ta fitar ita ce wacce ta shafi ka’idojin aikin hajji kawai, ba wai hana wasu kasashe shiga kasar ba.

Hukumar ta jaddada cewa masu dauke da visa na yawon bude ido ba su da damar gudanar da aikin hajji ko shiga birnin Makkah daga ranar 29 ga Afrilu zuwa 11 ga Yuni, 2025, kamar yadda dokokin aikin hajji suka tanada.

Advertisement

Wannan karin haske daga hukumomin Saudiyya ya kawar da rudani da damuwa da dama daga al’ummomin musulmi, musamman ‘yan Najeriya da ke shirin tafiya kasar domin ziyarar aikin hajii da  kuma  yawon bude ido.

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending