Connect with us

News

Saudiyya Ta Ki Yin Sulhu Da Isra’ila Sai An Bai Wa Falasdinawa ‘Yanci

Published

on

Yarima Farhan ya gaya wa Antony Blinken cewa Saudiyya tana yin abin da ta ga ya dace ne ba domin an tursasa mata ba.

DAGA MUHAMMAD MUHAMMAD ZAHRADDIN 

Saudiyya ta ce yana da muhimmanci ta kyautata dangantaka da Isra’ila mai makwabtaka “saboda ci-gaban yankin” amma hakan ba zai yiwu ba sai an tabbatar da “martaba da adalci” ga Falasdinawa.

Advertisement

Ministan Harkoki Wajen Saudiyya Yarima Faisal bin Farhan ne ya bayyana hakan yayin taron manema labarai da Sakataren Harkokin Wajen Amurka Antony Blinken wanda ke ziyara a kasar.

Jami’an Hukumar Kwastom 2,500 Na Karbar Horo Kan Shirin Zamanantar Da Kasuwanci Na TMP

“Idan ba a sama wa Falasdinawa zaman lafiya ba, idan ba a magance matsalolin da suke fama da su ba, duk wata kyautata alaka tana da iyaka,” in ji shi.

Advertisement

Yarima Farhan ya bai wa Amurka shawarar mayar da hankali wajen ganin an samu kasashe biyu – Isra’ila da Falasdinu – domin kuwa hakan ne zai zama adalci ga Falasdinawa.

Ya gaya wa Antony Blinken cewa Saudiyya tana yin abin da ta ga ya dace ne ba domin an tursasa mata ba.

Advertisement

“Idan ka ga mun yi wani abu, mun yi shi ne don radin kanmu kuma ba na tsammanin matsa lamba a kanmu zai taimaka,” in ji Yarima Farhan.

A gefe guda, Blinken ya yi kira ga Firaiministan Isra’ila Benjamin Netanyahu da kada ya yi kafar-ungulu a shirin samar da kasashe biyu – Isra’ila da Falasdinu – jim kadan bayan ya gama tattaunawa da Yarima Farhan.

Advertisement

Blinken ya yi magana ta wayar tarho da Netanyahu domin tattaunawa kan “kyautata dangantakar Isra’ila da Gabas ta Tsakiya ta hanyar inganta zaman lafiya da kasashen yankin,” a cewar kakakin Ma’aikatar Wajen kasar Matthew Miller.

 

Advertisement

 

TRT Afrika

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending