News
Tapswap, Notcoin, Hamstar, Kombat Poppo: Kadan Daga Cikin Illolin Mainin Ga Rayuwar Matasa Duba Da Yadda Su Ka Mai Da Hankali
Daga Muhammad Muhammad Zahraddin
Tun bayan fashewar Notcoins, matasa a Najeriya suka mayar da hankalai wajen yin mainin, domin tara maki ko ‘points’ a cikin manhajojin da suke amfani da su a wayoyinsu.
Daga lokacin ne kuma harkar kirifto ke ƙara samun karɓuwa a wajan matasa inda a kowace rana ake samun ƙaruwar ɓullar sabbin shafukan mainin da ke alƙawarta samar wa mutane kuɗi.
Fitattu daga ciki sun haɗa da Notcoins da Tapswap da Hamstar Kombat da Poppo da sauransu.
Gutsiri Tsoma Na Cigaba Da Tashi A Jam’iyyar APC Kan Gazawar Ganduje
Dan haka Yakamata Mahukunta su magantu akan halin da matasa su ka tsinci kan su a ciki, domin wannan babbar matsala ce ga rayuwar matasa kuma matsala mai tarin yawa duba da yadda su ka Mai da hankali akan mainin
Haka zalika harkar mainin b Mazan ba baga Matan ba kama daga kan Dalibai, Yan Kasuwa d kuma wadanda ma ba sa zuwa Ko Ina a koda Yaushe su na zaune a cikin unguwannin su kuma zuba mu su idanu da Gwamnati tayi hakan ba karamar matsala zai hai farmana ba a nan gaba.
Kadan daga cikin matsalolin sune:-
1 Yana hana su yin wani abu da zai fishshe su a nan gaba.
2 Yana hana su yin ibada akan lokaci.
3 Daliban cikin su kuma yana hana su mai da hankali a karatun su musammam ma ga ma su kwana a makaranta (Hostel).
4 Za su wayi gari ba su iya kowace Sana,a ba a lokacin da shekarun su ya huce na koyan Sana,ar, wanda hakan kuma zai iya sa su fadawa munanan ayyuka.
5 Kullun su na rayuwa akan igiyar zato wanda hakan ya ke sa su su ke barin ayyukan su na gaskiya su ke komawa kan abun da ba su da tabbaci.
6 Idan ma minin din gaskiya ne toh koda sun samu kudin fasikanci ne zai kara yaduwa a cikin Al, umma sana diyar samun kudin dangane da wasun su daga cikin su.
Dan haka mu na kira ga Mahukunta da kuma Malamai Magada Annabawa da su yi duba na tsanaki akan abun da mu ka fada domin ceto rayuwar Yan uwan mu matasa da kuma samar da gobe mai kyau ga rayuwar Al, ummar mu.
DAGA Comr Abba Alra-iwas
Comr Fatihu Adam Dandago
Hon Baffa Gwarzo
-
Opinion5 days ago
Wakilcin Mataimakin Gwamna Garo A Taron Tsaro Na Arewacin Najeriya Abin A Yabawa Gwamna Yusuf Ne
-
News7 days ago
Wasu Da Ake Zargi ‘Yan ISWAP Ne Da Iyalansu Sun Mika Wuya Ga Dakarun Soji
-
News1 day ago
Karuwar Ta’ammuli Da Miyagun Ƙwayoyi Tsakanin Mata Na Barazana Ga Makomar Iyali – Masana
