Connect with us

Politics

Gutsiri Tsoma Na Cigaba Da Tashi  A Jam’iyyar APC Kan Gazawar Ganduje

Published

on

Shugaban Jam’iyyar APC Na Kasa, Dakta Abdullahi Umar Ganduje,
Spread the love

DAGA MUHAMMAD MUHAMMAD YASIR 

Gutsiri tsoma na cigaba da tashi a jam’iyyar APC kan gazawar shugaban jam’iyyar na kasa, Dakta Abdullahi Umar Ganduje, wajen gudanar da taron majalisar zartarwa da kwamitin gudanarwa na kasa (NEC).

Jaridar Daily Trust ta ruwaito cewa Duk da irin muhimmanci da sassan biyu na jam’iyyar ke da shi wajen daidaitawa da kuma tabbatar da hukuncin da kwamitin ayyuka na kasa (NWC) ya yanke, musamman ma hukumar zabe mai zaman kanta ta ƙasa, wadda ita ce mafi girma ta biyu wajen yanke hukunci.

Advertisement

Majiyoyi daga jam’iyyar APC, sun ce baya ga gaza yin taron jam’iyyar na kasa da na NEC har yanzu ba a kafa majalisar ba da shawara ta jam’iyyar ta kasa ba duk da kasancewarta kungiyar dattawan masu faɗa a ji da ake sa ran za su tsawatar a jam’iyyar kamar Hukumar Amintattu (BoT) da ake da su .

Haka zalika Wikki Times ta ruwaito cewa Bincike ya nuna cewa tun lokacin da aka naɗa Ganduje a matsayin shugaban jam’iyyar a taron NEC da ya gudana a ranar 3 ga watan Agustan 2023 ba a sake irin wannan zama ba sai dai hukumar NWC ce kaɗai ke ƙoƙarin gudanar da zama yayin da sauran suka zama kamar ƴan kallo.

Advertisement

Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *