News
GOMBE: Akwai Unguwar Da Ba A Kai Gawa Makabarta A Mota
Mazauna Unguwar Afghanistan da ke Mazabar Garko a Ƙaramar Hukumar Akko ta Jihar Gombe sun bayyana damuwa kan rashin ingantacciyar hanya da gada, lamarin da suka ce na jefa rayuwarsu cikin mawuyacin hali tare da hana su samun sauƙin kai marasa lafiya asibiti da kuma kai gawa makabarta.
Al’ummar yankin sun ce tsawon shekaru suna gudanar da rayuwa cikin ƙalubale sakamakon rashin muhimman abubuwan more rayuwa, inda suka bayyana cewa su ne ke haɗa kuɗi domin gyara gadar katako da ke zama hanya ɗaya tilo ta shiga da fita daga unguwar.
FARASHIN AMINCI DA GASKIYA: Dalilin Da Yasa Kyakkyawan Aikin Mustapha Muhammad Ya Wuce Yabo
A cewarsu, duk lokacin da damina ta yi ƙarfi, ruwa kan yanke hanyar gaba ɗaya, abin da ke sa mazauna yankin shiga halin ƙaƙa-ni-ka-yi, musamman mata masu juna biyu, marasa lafiya, yara da tsofaffi.
Wani mazaunin yankin, Malam Saleh Maina, ya shaida cewa duk da koke-koken da suka dade suna kai wa gwamnati da wakilan jama’a, har yanzu ba a ɗauki wani gagarumin mataki ba domin magance matsalolin da suke fuskanta.
Ya ce a lokuta da dama mutane kan makale a hanya saboda ambaliyar ruwa, yayin da al’ummar yankin ke ci gaba da gyaran gadar ta hanyar gayya da tara kuɗi daga aljihunsu.
“Da zarar an yi ruwa mai yawa, shiga da fita daga unguwar na zama matsala. Wannan gadar da ake gani ma mu ne muke gyara ta saboda babu wani tallafi daga gwamnati,” in ji shi.
Maina ya kuma bayyana cewa duk da ci gaban da yankin ke samu da karuwar yawan jama’a, har yanzu ba su da ingantacciyar hanya, gada, asibiti, ruwan sha mai tsafta da kuma sauran abubuwan more rayuwa.
Ya ƙara da cewa sun taɓa miƙa koken al’ummar yankin ga ɗan majalisar da ke wakiltarsu, Musa Muhammad Wuro Biriji, domin kaiwa ga mahukunta, amma har yanzu ba su ga wani sauyi a aikace ba.
Shi ma ɗaya daga cikin masu kula da gyaran gadar, Isiyaku A. Dauda, wanda aka fi sani da Ziyara, ya ce idan al’ummar yankin ba su ci gaba da gyaran gadar ba, akwai yiwuwar ta rushe gaba ɗaya.
A cewarsa, gadar ita ce hanya kaɗai da ke haɗa yankin da sauran sassan gari, inda ya bayyana cewa ko gawar mamaci idan za a kai makabarta, sai an ɗauke ta a kafa saboda mota ba ta iya ratsawa.
“Mun shafe sama da shekara tara muna amfani da wannan gadar katako. Muna tara kuɗi gida-gida domin gyara ta, amma har yanzu ba mu samu wani tallafi daga gwamnati ba,” in ji Ziyara.
Ya ƙara da cewa domin a gyara gadar yadda ya kamata kafin damina ta tsananta, ana buƙatar sama da naira miliyan 1.5.
Mazauna yankin sun kuma nuna damuwa kan rashin asibiti da ruwan sha mai tsafta, suna masu cewa hakan na ƙara tsananta matsin rayuwar da suke fuskanta.
Ibrahim Usman, wani mazaunin yankin, ya ce marasa lafiya kan shiga haɗari musamman idan aka samu larurar gaggawa da dare ko a lokacin damina, saboda rashin hanyar da mota za ta bi domin kai su asibiti.
A nasa bangaren, Mai Unguwar Afghanistan, Muhammad Bello Banbulasta, ya ce sama da mutum dubu huɗu ne ke zaune a yankin, amma har yanzu ba su samu cikakkiyar kulawar gwamnati ba.
Ya bayyana cewa mata masu juna biyu na daga cikin waɗanda suka fi shan wahala sakamakon matsalar hanyar da gadar.
“Akwai lokacin da wani direban adaidaita sahu ya faɗa daga gadar yayin da yake ƙoƙarin kai wata mata mai ciki asibiti, lamarin da ya jawo asarar rai,” in ji shi cikin jimami.
Banbulasta ya kuma ce har yanzu yankin ba shi da rumfar zaɓe ko akwatin zaɓe, abin da ya sa suke ganin ba a bai wa yankin kulawar da ta dace ba.
Ya yi kira ga Gwamnatin Jihar Gombe da wakilan jama’a da su gaggauta samar da gada mai inganci, hanyoyi da sauran abubuwan more rayuwa domin rage wa mazauna yankin wahalhalun da suke fuskanta.
“Abin da muke nema ba alfarma ba ne. Muna neman a ba mu haƙƙinmu a matsayin ’yan ƙasa,” in ji Mai Unguwar.
Sai dai ƙoƙarin jin ta bakin ɗan Majalisar Dokokin Jihar Gombe mai wakiltar yankin, Musa Wuro Biriji, bai yi nasara ba. Haka kuma ba a samu jin matsayar Ma’aikatar Ayyuka da Muhalli ta jihar ba, sakamakon rashin kwamishinoni a halin yanzu.
