News
Kano: Rasuwar Hajiya Hadiza Ta Jefa ‘Yan Jarida Cikin Alhini
Al’ummar kafafen yaɗa labarai a Jihar Kano sun shiga jimami bayan rasuwar Hajiya Hadiza, fitacciyar mai sana’ar sayar da abinci a harabar Cibiyar ‘Yan Jarida (Press Centre), wadda ta rasu da safiyar Litinin bayan gajeruwar rashin lafiya.
Rasuwar tata ta girgiza ‘yan jarida, ma’aikatan kafafen yaɗa labarai da sauran masu hulɗa da ita, inda labarin mutuwarta ya bazu cikin gaggawa a Press Centre da sauran wuraren da ke kewaye.
Marigayiyar ta shahara wajen kyakkyawar mu’amala, karamci da kuma jajircewa wajen gudanar da sana’arta, lamarin da ya sa ta zama sananniya kuma abar ƙauna a tsakanin ‘yan jarida da jama’ar da ke ziyartar cibiyar.
Rasuwarta wani babban rashi ga al’ummar Press Centre, duba da irin gudunmawar da ta bayar tsawon kusan shekaru 20 tana hidimtawa ‘yan jarida da sauran jama’a.
A cewarsu, wajen sayar da abincinta ya zama tamkar wata mahadar sada zumunci, inda ‘yan jarida, editoci da baƙi ke taruwa domin cin abinci, tattaunawa da musayar ra’ayoyi yayin gudanar da ayyukansu na yau da kullum.
Baya ga sana’arta, Hajiya Hadiza ta yi fice wajen tallafa wa mata matasa ta hanyar samar musu da ayyukan yi da koyar da dabarun sana’a, abin da ya taimaka wa da dama daga cikinsu wajen samun hanyar dogaro da kai.
Wasu daga cikin ‘yan jaridar da suka yi magana kan rasuwar tata sun tuna da halayenta na kirki, tausayi da kuma yadda take karɓar kowa hannu bibbiyu ba tare da nuna bambanci ba.
Mambobin Ƙungiyar ‘Yan Jarida ta Najeriya (NUJ) da ke Press Centre sun bayyana marigayiyar a matsayin wani ginshiƙi na al’ummar cibiyar, suna masu cewa gudunmawar da ta bayar wajen ƙarfafa zumunci da haɗin kai ba za a manta da ita ba.
Sun yi addu’ar Allah Maɗaukakin Sarki Ya gafarta mata, Ya sanya ta cikin Aljannatul Firdausi, tare da bai wa iyalanta, abokanta da daukacin al’ummar Press Centre haƙurin jure wannan babban rashi.
