Connect with us

News

Gwamnan Jigawa Ya Dakatar Da Hadimansa  Guda 4 

Published

on

Jigawa

Gwamnan Jihar Jigawa, Malam Umar Namadi, ya dakatar da wasu hadimansa huɗu daga gudanar da ayyukansu har sai an kammala wasu matakai da gwamnatin jihar ke ganin sun dace.

Dakatarwar, wadda ta fara aiki nan take, na ƙunshe ne cikin wata sanarwa da Sakataren Gwamnatin Jihar, Malam Bala Ibrahim, ya fitar a ranar Litinin.

Advertisement

Hadiman da abin ya shafa sun haɗa da Abbas Makama, Babban Mataimaki na Musamman kan Kula da Ambaliyar Ruwa; Salisu Muhammad, wanda aka fi sani da Rosy Auyo, Mataimaki na Musamman kan Harkokin Kasuwanci; Ibrahim Yunusa, Mataimaki na Musamman kan Sa-Ido a Fannin Ilimin Firamare; da Umar Abdulkadir (Alhaji Bullet Auyo), Mataimaki na Musamman kan Harkokin Noma.

Sai dai sanarwar gwamnatin ba ta yi ƙarin haske kan takamaiman dalilan da suka haifar da dakatarwar ba, illa dai ta tabbatar da cewa matakin ya fara aiki ne daga ranar da aka sanar da shi.

Advertisement

Gwamnatin jihar ta kuma bayyana cewa dakatarwar za ta ci gaba da aiki har sai an fitar da wani sabon umarni dangane da lamarin.

Matakin ya jawo ce-ce-ku-ce a tsakanin al’umma da masu ruwa da tsaki a jihar, yayin da ake jiran ƙarin bayani daga mahukunta kan abin da ya haddasa dakatarwar da kuma matakan da za a ɗauka a gaba.

Advertisement

 

 

Advertisement

AMINIYA

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending