Politics
Ba Wanda Zai Iya Kayar Da Tinubu A Zaben 2027 Sai Dan Arewa —Dele Momodu

Tsohon dan takarar shugaban kasa kuma jigo a jam’iyyar PDP, Dele Momodu, ya ce babu wani dan kudu da zai iya kayar da Shugaba Bola Ahmed Tinubu a zaben shugaban kasa na 2027, face dan Arewa da ya shahara kuma yake da karbuwa a kasa.
Momodu ya bayyana haka ne a wata hira da ya yi da Arise TV a ranar Laraba, inda ya bayyana cewa lamarin siyasa a Najeriya na bukatar tsari da dabarun fahimtar juna da hada kai.
Ranar Ma’aikata: “Muna Cikin Matsin Rayuwa” — Ma’aikatan Najeriya
Ya ce, “Ina ganin dan Arewa ne kadai zai iya fuskantar Tinubu. Idan wani dan kudu yana tunanin zai iya kayar da shi, to yana bata lokaci ne kawai. PDP ko wata kawance ba za su iya samun nasara ba idan suka tsaya da dan kudu.”
A cewarsa, yankin Arewa na jin cewa gwamnatin Tinubu tana fifita Kudu a kan Arewacin Najeriya, kuma wannan jin haushi na iya zame wa ‘yan adawa dama ta tunkarar gwamnati a zaben mai zuwa.
Ya bayyana cewa dan takara irin su Sanata Rabiu Musa Kwankwaso zai iya zama jigon da za a hada kai da shi domin fuskantar Tinubu a 2027.
“PDP tana cikin rikici. Wasu daga cikin mambobinta suna kokarin kafa kawance da wasu jam’iyyu, yayin da wasu suka nace sai jam’iyyar. Wannan na kawo rudani a cikin jam’iyyar,” in ji shi.
Momodu ya kara da cewa idan PDP ta ki sauyawa da sabunta kanta, to za ta iya bacewa kamar yadda wasu tsoffin jam’iyyu suka bace.
“Dubin tarihi, UPN, NPN da AD sun bace saboda rashin sabuntawa. Haka ma PDP za ta iya fada wannan hali idan ba ta tashi tsaye ba,” in ji shi.
A kan jita-jitar cewa Atiku Abubakar zai koma jam’iyyar APC, Momodu ya ce hakan ba zai yiwu ba, yana mai cewa APC kanta na fama da rikicin cikin gida da rashin daidaito.
“Wannan maganar Atiku zai koma APC karya ce. APC ma da kanta tana fama da rikici, ba za ta iya shawo kan matsalolinta ba,” in ji shi.